Kammala zaman majalisar Najeriya ta tara
June 8, 2023Shekaru hudu cur suka dauka suna wannan aiki na majalisa aikin da a yanzu yazo karshe, wanda shine ginshiki na uku a tsarin dimukurdiyyar Najeriya. Aikin da ya shafi kafa sabbin dokoki da yiwa wadanda ake da su gyaran fuska domin dacewa da zamani. Majalisa ta tara ta kasance wacce ta samu kyakyawar fahimtar juna tsanakinta da bangaren zartaswa wato shugaban Najeriya ke nan, wannan ya taimaka wajen samun nasara da saukin tafiyar da aiki. Sanata Ahmed Lawal shi ne shugaban majalisar datawan Najeriyar da ta kamala wa'adinta.
Karin Bayani: Majalisa ta nemi hukunta badakalar jirgin Nigeria Air
Majalisa ta tara ta bullo da sabon tsari na amincewa da kasafin kudi kafin shekara ta kare domin bada dama wajen aiwatar da shi a tsakanin watan Janiaru zuwa Disamba na kowace shekara. Wannan ya rage jan in ja da ake samu a tsakanin majalisar da bangaren zartsawa da ta kaiga kiran ‘yan majalisar ta tara ‘yan amshin shata. Hon Bello Kaoje dan majalisar wakilan Najeriya ne a majalisa ta tara ya ce batun akwai rashin fahimta.
To sai dai duk da samun nasara na amincewa da dokoki 112 ciki har da dokokin da suka dade ana jan kafa a kansu irin dokar saka fasakin harakar man fetur a Najeriya. Gaza samun nasarar dokar bai wa kanana hukumomi ‘yan cin gashin kansu babban koma baya ne.
Duk da doki da ma zarya na neman shugabancin majalisa ta 10 da za a kaddamar da ita a mako mai zuwa, kwararru na bayyana akwai sauran aiki a gaba, domin fiye da rabin ‘yan majalisar sabbi ne abin da ke kawo koma baya ga aikin majalisa domin kuwa dole sai sun yi tatata kafin su mike.