1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ko CEDEAO: Ba takunkumi ga Mali

October 7, 2020

A wani abun da ke zaman alamun sabon babi a cikin rikici na siyasa ta kasar Mali, kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ta dage takunkumin da ta dorawa kasar bayan sojoji sun yi juyin mulki.

https://p.dw.com/p/3jZym
Moctar Ouane | Ernennung zum Interims-Premierminister von Mali
Sabon firaministan kasar Mali Moctar OuaneHoto: Raveendran/AFP/Getty Images

Cikin watan Augustan wannan shekarar ne dai, sojojin suka yi juyin mulki a Malin, abin kuma da ya sanya kasar ta fuskanci  jerin takunkumi, ciki kuwa har da na kungiyar ta Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, wato ECOWAS ko CEDEAO. Sai dai kuma cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun shugaban kasar Ghana kuma shugaban kungiyar ta  ECOWAS ko CEDEAO, Nana Akuffor Addo da ta yi karin haske kan cire takunkumin, ta ce hakan ya zama wajibi, bayan da sojojin da suka yi juyin mulki a Malin, suka cika sharuddan kungiyar. 

Karin Bayani: Mali: Za a nada gwamnatin rikon kwarya

Sojojin dai sun yi nasarar nada sabon shugaban kasa da firminstan da zai jagoranci kokarin mayar da kasar bisa turba ta dimukuradiyya cikin watanni 18 da ke tafe. Kasashen na ECOWAS ko CEDEAO din dai, sun kuma nemi agaji da goyon baya ga sabuwar gwamnatin da ke a Bamakon wajen tabbatar da nasarar shirin da ke da zummar kai wa ya zuwa karbabben zabe a kasar.

Mali politische Krise | Videokonferenz westafrikanische Führer
Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta cirewa Mali takunkumiHoto: Reuters/Ecowas

Matakin EOCOWAS ko CEDEAO din dai ya kai karshen kiki kakar da ta dauki a hankali cikin yankin da ma a wajensa, kuma ta mai da Malin kasa ta farko da ta sake komawa bisa ikon sojoji a cikin yankin na yammacin Afirka. Ana kuma kallon nasarar a matsayin aiken sako a cikin yankin, na tabbatar da kai karshen tasirin soja a cikin harkokin mulki na kasashen ECOWAS ko CEDEAO din 15 da kila tabbatar da tsarin na dimukuradiyya komai rauni.

To sai dai kuma kalubalen da ke gaban masu ruwa da tsaki da makomar ta Mali dai, na zaman iya kai wa ga tabbatar da karbabben tsari cikin kasar da ta fuskanci juyin mulkin soja guda biyu a tsawon kasa da shekaru takwas. To sai dai kuma a fadar Farfesa Sadiq Abba da ke zaman masani na siyasar yankin na Afirka ta Yamma, cika umarnin ECOWAS ko CEDEAO a bangare na sojan Mali, na nuna irin imani da tabbatar da ingantacciyar makoma ga kasar.

Karin Bayani: Rikicin Mali: ECOWAS ta dauki matakai

Sai dai ko ma ya zuwa ina sojojin ke iya kai wa da nufin burge 'yan kasar da ma makwabtan Malin a bisa kokari na tabbatar da sabon tsarin dimukuradiyya a kasar dai, daga dukkan alamu daukaci na kasar na bukatar agaji da nufin tunkarar jerin matsaloli na tattali na arziki dama tsaro.

Karin Bayani: Kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Mali

Kusan biyu a cikin uku na kasar dai na a karkashin iko na masu daukar makamai, abin kuma da ke nufin takaitaccen tsari na samar da ingantaccen shugabancin al'umma a kasar. Kabir Adamu dai na zaman masani a harkar ta tsaro, kuma a fadarsa cire takunkumin na iya babban tasiri ga makomar Malin. Ingancin lamura a cikin Malin dai na da babban tasiri a daukacin yankin sahel dama ragowar kasashen Ecowas dake dada kallon rigingimu iri iri a cikinsu.