Sojoji sun sake dage babban zabe a Mali
September 28, 2023Gwamnatin mulkin sojan Malin dai ta bayyana cewa ta dage zabukan na ranar 24 ga watan Fabarairun 2024 ne, saboda wasu gyare-gyare da take yi. Sai dai manazarta na hasahen cewar da wuya rashin tsaro ya bari a gudanar da zabukan. Wannan dai wani sabon jinkiri ne da aka samu a zaben, bayan alkawuran da ta dauka sakamakon matsin lamba daga kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO. Tun farko an shirya yin zagaye na farko na zaben a ranar hudu ga watan Fabarairu shekara ta 2024, kana a yi zagaye na biyu a ranar 18 ga watan. Sojojin sun yi juyin mulki har sau biyu a Mali cikin kasa da shekara guda, wato a watan Agusta na 2020 da kuma watan Mayu 2021.
Tun da fari sun ce za su mika mulki ga farar hula a shekara ta 2022, amma a karshen shekarar ta 2021 gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Kanal Assimi Goïta ta sanar da cewa ba za ta iya mutunta jadawalin da aka amince da shi da ECOWAS ko CEDEAO din ba. A cewarta tana tunanin kasancewa kan mulkin har zuwa tsawon wasu shekaru biyar, sai dai dalilan da gwamnatin ta bayyar kan dage zaben ba su gamsar ba. Yanzu haka dai kasar ta Mali na rasa sassa da dama na kasarta sakamakon yadda masu ikirarin jihadi suka katse hanyoyin da ke kai wa zuwa birnin Timbuktu da kewaye na arewacin kasar, abin da ya jefa dubban mazauna yankin cikin mayuwacin hali. A yankuna da dama na kasar ma, 'yan ta'addan na dada kai hare-hare. A halin da ake ciki gwamnatin rikon kwaryar Malin, ta ce nan gaba za ta bayyana sababbin ranakun zaben bayan tattaunawa da Hukumar Zaben Kasar.