1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Manchester na zawarcin Amorim don maye gurbin Ten Hag

October 29, 2024

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na tattaunawa da mai horas da 'yan wasa na kasar Portugal Ruben Amorim domin kasancewa sabon manajan kungiyar bayan sallamar Erik ten Hag sakamakon rashin nasara a wannan kaka.

https://p.dw.com/p/4mKik
Mai horas da 'yan wasa na kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon na Portugal, Ruben Amorim a yayin da yake bada umarni a wasan Lisbon da Benfica
Mai horas da 'yan wasa na kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon na Portugal, Ruben Amorim a yayin da yake bada umarni a wasan Lisbon da BenficaHoto: Joao Rico/DeFodi Images/picture alliance

Wasu kafofin yada labaran Burtaniya sun rawaito cewa kungiyar ta Manchester United na bukatar matashin mai horas da 'yan wasa na Sporting Lisbon 'dan shekara 39 domin ya jagoranci kungiyar a matsayinsa na matashi mai jin jini a jika, biyo bayan rashin nasarar da kungiyar ke fuskanta a wannan kaka 2024/2025.

Karin bayani: Wasanni: An caskara Manchester United

A farkon wannan shekara 2024, kungiyar kwallon kafar Ingila ta Liverpool ta so ta dauki Amorim bayan ficewar Jurgen Klopp, amma daga bisani ta canza ra'ayi inda ta rattaba hannu a kan kwantaragi da cociyan kasar Holland Arne Slot.