Masar ta yi nasarar kawar da cutar zazzabin cizon sauro: WHO
October 20, 2024Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewar Masar ta yi nasarar kawar da cutar zazzabin cizon sauro kwata-kwata daga fadin kasar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Geneva, shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya danganta wannan mataki da wani rukuni na tarihi saboda sadaukar da kai da al'ummar Masar da gwamnatin kasar suka yi wajen ganin bayan Maleriya. A halin yanzu dai, kasashe 44 na duniya da kuma yanki daya ne suka ja wa zazzabin cizon sauro birki.
Karin bayani: Najerriya: Yaki da cutar zazzabin cizon sauro
Abin sani a nan shi ne, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na ba da takardar shaidar kawar da cutarzazzabin cizon sauro a lokacin da wata gwamnati ta yi nasarar katse hanyoyin yada Maleriya a kasar na kalla shekaru uku a jere. Sannan kuma ya zama wajibi a kan wannan kasa ta yi amfani da dabarunta wajen hana farfado da hanyar sake yada cutar. A cewar WHO, zazzabin cizon sauro na kashe mutane sama da 600,000 a kowace shekara, inda kashi 95% na wadanda suke kamuwa da ita ke rayuwa a Afirka.