Fadada matakin shigo da abinci
October 13, 2023Wata sanarwar Babban Bankin tarrayar Najeriya na CBN dai ta ce ta dage haramcin da ke kan wasu nau'o'in kayan abinci da bukatu na rayuwa 43. Kuma kama daga shinkafa ya zuwa nama ko bayan masara da tsinke na sakace dai, a fadar bankin 'yan kasar suna da damar samun dala domin shigo da jerin kayan.
Karin Bayani: Najeriya: Kokarin magance matsalar karancin abinci
Babban burin bankin dai na zaman rage matsi bisa bukata ta kudin Dalar (Amirka) da ke ta karuwa a bayan fage da kuma ta dau kudin kasar zuwa matsayin ban tsoro. Ya zuwa yanzun dai Naira da ta haura dubu bisa kowace Dalar Amirka guda daya. To sai dai kuma Najeriya tana tsakanin wadatar da Dalar domin bukatu na masu shigo da kaya da kuma kare miliyoyi na aiyukan da kasar ta yi nasarar samarwa a shekaru takwas na ci da kai da ke zaman babban kwazo.
A lokaci kankani dai Najeriyar tai nasarar tashi daga kasa ta kan gaba a nahiyar Africa wajen shigar shinkafa yar Thailand ya zuwa ta farkon fari a cikin noman shinkafar da samar da aiyyuka cikin masana'antar sarrafa shinkafar. Wata kiddidgar da bata da tabbas dai tace aiyyuka musan miliyan 12 ne suka fito daga noma da sarrafar shinkafar a shekaru takwas na tsohuwara gwamnatin ta tsohon Shugaba Muhammdu Buhari. Mr Peter Dama dai na zaman shugaban kungiyar kananan masu sarrafa shinkafa a cikin Najeriya da kuma ya ce abin da ke akwai a halin yanzu na zaman bala'i babba a cikin masana'antar shinkafar.
Hauhawa ta farashin da ta kalli buhun shinkafar haura Naira dubu Hamsin a karon farko a cikin tarihi, ya jefa masu mulkin kasar cikin tsaka mai wahalar gaske. Abujar dai tana a tsakanin wadatuwa ta abinci a cikin tsanani na matsi da kuma dorawa a cikin bakar wuya ta ci da kai tsakanin mutane.