Matsalolin tafiye-tafiye tsakanin Nijar da Najeriya
January 21, 2025Kimanin kwanaki hudu ke nan da direbobi da kuma fasinjoji ‘yan Najeriya masu son shiga Jamhuriyar Nijar ba su ji da dadin binciken kwakwaf da ake musu wanda ba sabon ba a wurinsu. Direbobi wasu ma sun hakura sun ajiye motocinsu.Fasinjoji wasu sun hakura sun daina tafiya sai sun ji abin da hali ake ciki. A cikin fasinja guda goma za a ga ‘yan Nijar kwaya takwas ne ‘yan Najeriya kwaya biyu, saboda haka tafiya ta ragu. Idan da ana yin mota goma to za ka ga bai wuce a yi mota uku ba ko biyu a wuni sakamakon rashin tafiye-tafiye da ake yanzu.
Karin Bayani: Sabon zargin Nijar ga makwanbtanta da Faransa
Akwai dai maganganu da dama dangane da ‘yan Najeriya da ke shiga Jamhuriyar Nijar a tsawon wadannan kwanaki. Alhaji Aminu mataimakin sakataren kungiyar direbobi ne ta Nigeria da ya saba lodin Zinder. Ya ce abubuwan suna ci masa tuwo a kwarya a tafiya Zinder tun daga kan Tinkim a kan iyaka. Na farko dai fasinja za su sauka ko da suna da takardu idan dai kai dan Najeriya ne sai ka ba da jaka 15, idan ka ba da jaka 15 takardar 300 za a yi ma. Najeriya da Jamhuriyar Nijar mu'amalolin al'umominsu na sada zumunci ne ko auratayya da cinikayya ba sa tsananta amfani da takardu, to sai dai sarki goma zamani goma ne.
Wanda duk zai yi tafiya tsakanin Jamhuriyar Nijar da Najeriya ka da ya yi la'akari da masu magana a cikin kafofin labarai na surutan babu gaira ba dalili. Da wanda zai yi dan Nijar da wanda zai yi dan Najeriya, shi dai tafiya ta kama shi to ya rike hujjarsa ta yin tafiya.
Duk da cewa passport da katin dan kasa hakki ne na dan kasa da ya kamata ya same su, amma za a jima wasu ba su mallake su ba.