Buhari ya gana da gwamnan Imo kan matsalar tsaro
April 19, 2022Babu zato ba kuma tsammani dai wasu 'yan bindiga cikin jihar Imo suka kashe wasu jami'an hukumar zabe da ke aiki na rijistar 'yan zabe na shekarar badi. Abin da kuma da ya tada hankali cikin jihar dama a waje ya kuma kai ya zuwa wata ganawa a tsakani na shugaban kasar da gwamna na jihar a cikin neman mafita.
Karin Bayani:Najeriya: Mabanbantan ra'ayi kan sojan haya
Harin da ke zama na baya dai na kara fitowa fili da irin jan aikin da ke gaban mahukunta na kasar da ke fatan kwantar da hankula ya zuwa babban zaben kasar na shekarar badi.
A baya dai yankin ya kalli karuwa ta ta da hankalin da ya kalli kona cibiyoyin zabe da ragowar kayan aiki a sassa dabam-dabam cikin yankin na Kudu maso gabas. Hope Uzodinma dai na zaman gwamnan jihar Imo da kuma ya ce an yi nasarar kamen kimanin mutane guda biyu a cikin masu kisan. Inda yake cewa zahiri ma dai sun so su kai hari ne bisa gidan yarin da ke garin Okwige, amma sai aka samu bayanan sirri, kuma aka kara jami'an tsaro.
A cikin wannan mako ne dai aka tsara wani babban taro na hafsoshi na jami'an tsaron kasarda nufin sake nazari na dabarun tunkarar rashin tsaron walau a yankin na gabas ko kuma arewa maso yammacin kasar da ke dada kallon karuwa na barayin daji. Tuni dai gwamnatin kasar ta ce ta sayi karin makamai na zamani domin tunkarar matsalar da ko bayan rashin tsaron ke neman jawo matsala har a cikin tsarin zabe na kasar.
To sai dai kuma a fadar Dr Rabi'u Musa Kwankwaso da ke zaman tsohon ministan tsaron kasarkuma jagoran jam'iyyar NNPP ta kasar gazawar su kansu sojojin kasar na neman jefa kasar cikin tsaka mai wuyar gaske. Abin jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa cikin kasar da ke shirin kaddamar da yakin neman zabe a cikin rudanin rashin tsaron.