Ana zargin Rasha da tallafa wa Hamas
November 6, 2023Amirka da manyan kasashe ake zargi da galibin tashe-tashen hankula yayin da Rasha kuma take nuna kanta a matsayin mai neman zaman lafiya, kuma duk abin daRashatake yi ko kuma 'yan ta'adda a wasu bangarori na duniya da suka hada da Gabas ta Tsakiya duk sai an zargi Amirka. Duk da haka ba shi ne gaskiyar abin da yake faruwa ba, amma Rasha tana ci gaba da amfana a haka, inda rikicin yankin Gabas ta Tsakiya da ya barke ana ganin Rasha tana cin gajiyar abin da ke faruwa. Ruslan Sulejmanov masanin Gabas ta Tsakiya yana ganin Rasha tana kara kusantanChinadomin samun yanayin da zai yi ma ta dadi, kuma sabon rikicin zai taimaki Rasha wajen rage masu saka mata ido sannan ya ci gaba da cewa:
Akwai masu ganin lokaci ne da Rasha za ta nuna kusanta da kasashe Musulmai
''Rasha tana nata yakin. Masu adawa da Rasha sune kasashen Yamma da ke goyon bayan Ukraine. Domin haka idan sun samu wani yakin da ya kawar musu da kai haka zai zama abin da Rasha take bukata. Wannan zai kassara masu adawa da fadar Kremlin, da kara kassara masu goyon bayan Ukraine kuma yanzu ba za su mayar da hankali zuwa kan Ukraine ba." Akwai masu ganin lokaci ne da Rasha za ta nuna kusanta da kasashen Musulmai, kuma mahukuntan birnin Moscow suna shirye da yin haka, saboda duniya ba ta batun Ukraine, amma sai Isra'ila. Sai dai a fili yake babu dangantaka tsakanin yake-yaken guda biyu da yanzu haka suke wakana. Konstantin Pachaljuk masanin siyasa wanda ba da jimawa ba ya koma zuwa Isra'ila zama, yana gani koyaushe ana neman daura laifin da ke faruwa ne kan kasashe Yamma maimakon duba lamarin da idon basira:
Yaki na yin barazna ga mamaye yankin Gabas ta Tsakiya a kan idon duniya
"Duba kowa kowa yana mayar da hankali kan Ukraine a farkon yakin. A Isra'ila lamura sun rikice, kuma lamarin da ke faruwana ci gaba neman cinye yankin Gabas ta Tsakiya. Domin haka akwai babbar barazanar yaki. Kuma kasashen Yamma za a daura wa laifi. To mene ne za a yi idan an zargi rasha? Wadanda suka san abin da yake faruwa ba za su daura mana laifi ba."Kutsawa da mutane suka yi filin jirgin saman Dagestan sakamakon jirgin da ya fito daga Isra'ila da kara samun kyamar Yahudawa a wasu yankunan Rasha masu yawan Musulmai na kara zama matsalolin tsaro ga mahukuntan Rasha wajen tabbatar da doka da oda a yankunan. Michail Krutichin masanin siyasa da tattalin arziki dan Rasha wanda yanzu haka yake kasar Norway yana ganin yakin na yankin Gabas ta Tsakiya na kara kassara kasar Rasha.