1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Babban Zauren MDD na tattauna rikicin Gaza

Abdullahi Tanko Bala
October 26, 2023

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na tattauna halin da ake ciki a zirin Gaza a wani zama na musamman yayin da aka kasa cimma matsaya kan yakin a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar

https://p.dw.com/p/4Y4sp
New York | Der chinesische Vizepräsident Han Zheng spricht vor der Generalversammlung der Vereinten Nationen
Hoto: Mary Altaffer/AP/picture alliance

A jawabinsa ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian ya yi kashedin cewa idan Israila ba ta dakatar da hare haren ramuwar gayya da ta yi a kan kungiyar Hamas ta Falasdinawa a yankin zirin Gaza ba, to kuwa Amurka ba za tsira daga wannan guguwar ba.

Ana sa ran kada kuri'a a kan wani daftarin kudiri da kasar Jordan ta gabatar. Sai dai babu tabbas ko daftarin zai sami amincewa saboda ya yi kiran tsagaita wuta nan take da kuma wasu batutuwa wadanda masu goyon bayan Israila ba su amince da su ba.

 

Karin Bayani: Rikicin Israila da Gaza an kasa tsagaita wuta

A waje guda kuma masu lura da al'amura na fatan za a bai wa kasashe masu tasowa damar nesanta kansu daga Israila.

Kudirin babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniyar dai bai da karfin tilasta aiwatarwa sai dai yana da muhimmanci ne kawai don nuna cewa an yi wani abu a zahiri.

An kira taron ne saboda gazawar kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na kasa amincewa da daftari kan halin tagaiyara da al'umma ke ciki da kuma daukin jinkai a Gaza.