Ghana: Maza na yakar cin-zarafin mata
August 1, 2024Cin-zarafin mata da maza ke yi na zama babbar barazana da suke fuskanta a fadin kasar Ghana, inda kididdiga ke cewa daya a cikin mata hudu sun fuskanci cin-zarafi a zahiri ko yunkurin fyade. Ka'idojin al'adu da suke sa mata su zama masu biyayya ga maza, suna karfafa cin-zarafi a kansu. Kungiyoyi kamar ActionAid Ghana da kungiyar lauyoyin kasa da kasa, na shawo kan maza wajen yaki da cin-zarafin mata. Evans Aburgi na cikin wannan tafiya da nufin kawo gyara, inda ya ce a kullum yana zama da abokan tafiyarsa tare da wayar da kansu cewa, bai dace a rika cin-zarafin mata ba saboda tauye hakkin dan Adam ne.
A lokacin da aka yi kokarin cin-zalin mace ta fuskar lalata ko ma ta wace hanya, ba daidai ba ne. Ba kawai don ka auri mutum yana nufin zaka sadu da mace da karfin tuwo ba da ma sauran anu'o'in cin-zarafi. Yanzu haka dai maza a kasar Ghana, na kawo babban sauyi a zamantakewar maza da mata a matakin unguwa har zuwa ko ina. John Know shi ne shugaban kungiyar ActionAid a kasar Ghana, kuma a cewarsa aikin da suke yi ya isa ga matan da aka ci-zarafinsu maza da kananan yara a kasar. Kuma shirin yana sanya tunanin mutane kan cin-zarafin mata da yara, abinda a ya ce na nuna alamun hakarsu ta cimma ruwa.