1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAfirka

Me ya sa cutar kwalara ke karuwa a duniya?

Julia Vergin ZMA/MAB
September 26, 2023

Hukumar lafiya Duniya ta ce adadin masu kamuwa da cutar kwalara na karuwa a duniya. Cutar ta fi kamari a kasashe bakwai yawancinsu a nahiyar Afirka. Duk da cewa tana da saukin yaduwa, amma ana iya magance Kwalara.

https://p.dw.com/p/4Wpeo
Mozambik na daga cikin kasashen da ake yawan fama da kwalara
Mozambik na daga cikin kasashen da ake yawan fama da kwalaraHoto: Sitoi Lutxeque/DW

Adadin wadanda suka kamu da cutar kwalara a shekarar 2022 ya ninka idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, a cewar wani rahoto na baya-bayan nan da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar. A cikin 2021, WHO ta sami rahoton yawan wadanda suka kamu da cutar kwalara kusan 223,000 a duk duniya. A shekarar da ta biyo baya ta 2022 kuwa, an samu rahoron sama da mutane 472,000 da suka kamu da cutar a cikin kasashe 44 daban-daban.

Karin bayani:Ambaliya: Kwalara ta barke a Kamaru da Chadi 

Ba wai kawai adadin masu kamuwa da cutar ya karu ba, kamar yadda rahoton na WHO ya nuna, har ma girman barkewar cutar ya karu. Kasashe bakwai kowacce ta ba da rahoton bullar cutar kwalara sama da 10,000 a shekarar 2022, wadanda suka hada da Siriya da Afghanistan da Kamaru da Malawi daNajeriya da Somaliya da Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango.

Wadanda cutar kwalata ta sa aka kwantar da su a asibiti a Guinea-Bissau
Wadanda cutar kwalata ta sa aka kwantar da su a asibiti a Guinea-BissauHoto: DW

Dr. Daniel Unterweger, masanin ilimin halittu a jami'ar Kiel da ke nan Jamus ya ce: "Idan aka dubi adadin masu kamuwa da cutar kwalara a 2022, har yanzu yana kasa da wadda aka ruwaito kan cutar a cikin 2019 ko 2017."

Dr Unterweger ya ce kwayar cutar kwalara ba ta yawo ta iska ana shanta ne da baki, hakan kuma kan faru ne ta hanyar ruwan sha da aka gurbata da kwayoyin cutar. Ya ce: "Mutum na kamuwa da kwalara ne ta hanyar shan kwayoyin cutar da ke haddasa kwalara da baki, hakan na nufin cewa dole ne a samu abubuwa guda biyu: Na farko, kwayar cutar ta iya kasancewa a cikin muhalli, misali a cikin kogi, na biyu kuma mu'amalar mutum da wannan kogin, ta hanyar shan ruwan kogin alal misali."

Karin bayaKwalara na ci gaba da yin ta'addi a Najeriyani: 

Gurbataccen ruwa na cikin abubuwan da ke haddasa cutar kwalara
Gurbataccen ruwa na cikin abubuwan da ke haddasa cutar kwalaraHoto: AP

Mutanen da suka kamu da cutar na iya samun nasarar magancenta a mafi yawan lokuta ta hanyar amfani da ruwa  da aka gauraya da gishiri da sukari, wannan ita ce hanya mafi sauki na shawo kan kwalera inji Dr Unterweger: "Idan mutum ya kamu da cutar kwalera yana da zabin wannan magani, ba kasafai yake galabaitarwa ba balle ya kai ga mutuwa ba. Maganin yana taimakawa sosai, wajen samun waraka. A zahiri yana da matukar tasiri kan kaifin cutar kuma iya ceton rai daga gare ta saboda zaɓin magani."

Akwai kuma rigakafin da ake digawa ta baki wanda ke ba da kariya mai kyau na akalla 'yan shekaru. Duk da haka, WHO ta kiyasta cewa tsakanin mutane 21,000 zuwa 143,000 ne ke mutuwa a kowace shekara daga kamuwa da kwayar cutar kwalera mai haifar da amai da gudawa. Tsaftataccen ruwan sha shine mafi mahimmancin abin da ake bukata don rigakafin cututtukan kwalara.