1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Annobar kwalara a sansanin gudun hijira

November 14, 2018

Cutar Kwalara na ci gaba da haddasa hasarar rayukan jama’a a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihohin Borno da Yobe da Adamawa a cewar kungiyoyin kasa da kasa da ke aikin jinkai a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriyar.

https://p.dw.com/p/38GC0
Nigeria Stadt Borno State
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Cutar ta kwalara ta hallaka mutane 175 daga cikin mutane dubu goma da suka kamu a jihohin Adamawa da Borno da Yobe a farkon wannan watan Nuwamban kamar yadda Janet Cherono jami’ar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway ta bayyana a wata sanarwa da ofishin hukumar ya fitar

NIGERIA Hunger und Mangelernährung
Wasu 'yan gudun hijira a sansanin Maiduguri Hoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

A cewar hukumar wannan cuta na yaduwa a tsakanin sansaonin ‘yan gudun hijira a wadannan jihohin kamar wutar daji kuma abin tashin hankali babu isassun cibiyoyin kula da lafiya da za su kula da masu fama da cutar.

Ana fargabar samun karuwar mace-mace musamman na mata da yara da ke sansanin ‘yan gudun  hijirar saboda yadda ake samun Cunkoso da karancin tsabtataccen ruwan sha da kuma gurbatar muhalli, abubuwan da ke haifar da yaduwar cutar a sansanonin na ‘yan gudun hijira.

Masana harkokin kiwon lafiya kamar Dr Nasir Naseef sun shawarci mazauna wadannan wurare su dauki matakan rigakafi kafin matakai da hukukomi za su dauka na shawo kann cutar.