Me zaben Amurka ke nufi ga Afirka?
October 24, 2024Masana dai na ganin cewa duka 'yan takarar shugabancin Amurkan Kamala Harris da Donald Trump na bin wani tsarin ne da 'yan takarar shugabancin kasar ke da shi wanda al'ummar Afirka ke da masaniya a kansa. Babu wani a cikin 'yan takarar da ya mayar da alaka tsakanin Amurka da Afirka wani babban jigo da batun zaben. Trump da shugaban kasar mai barin gado Joe Biden ba su taba kai ziyara lokacin da suke kan karagar mulki ba, haka nan babu wani a cikinsu da ya mayar da hankalinsa a kan nahiyar.
Karin Bayani: Makomar Afirka a sabuwar gwamnatin Amirka
A hirar sa da tashar DW Cameron Hudson na cibiyar nazarin harkokin kasashen waje da ke birnin Washington na Amurka, ya nunar da cewa tsare-tsaren 'yan takarar na Democrats da Republicans kan nahiyar Afirka, ba su bambanta da juna sosai ba. A cewarsa Afirka ba ta daga cikin abubuwa masu muhimmanci sosai ga Amurka ya kara da cewa:
Karin Bayani: Barazanar yakin cacar baki tsakanin Amirka da China
"Mutane sun fara fahimta sannu a hankali Afirka ta fara zama wani yanki mai muhimmanci ga Amurka, inda aka yi la'akari da misali Tekun Bahar Maliya da za ka iya wucewa ta cikinsa da kuma na Atlantika, wanda hada kan iyaka da Amurka. Nahiyar kuma, na da kuri'u masu yawa a Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai ga alama, yayin da Amurka ta yi kokarin samun hadin kan baki da yan kasashen nahiyar lokacin kada kuri'ar yin tir da Rasha dangane da mamayar da ta yi a Ukraine, hakan ya rage muradun Amurka a nahiyar ya kuma rage tasirinta a duniya."
Karin Bayani: Amirka ta kori wasu kasashe daga cikin AGOA
Hudson din dai na ganin tasirin Chaina a Afirka, ka iya janyo ra'ayin Amurka. Amurka da Chaina dai, na kokarin ganin sun samu gagarumin tasiri a Afirka. Duk da cewa Amurka ce ta fi bai wa Afirka tallafi, sai dai Chaina ce babbar kawar nahiyar ta fuskar kasuwanci. Mai fashin baki a kan al'amuran siyasa a kasar Kenya Brian Singoro Wanyama na da ra'ayin cewa:
"Amurka na baya ta fuskar bunkasar kasuwanci a Afirka, hakan na nufin ya fi wa kasashen Afirka sauki su nemi tallafi daga Chaina ko Rasha. Ya fi musu saukin su samu tallafi daga kasashen gabashi, maimakon daga Amurka."
Karin Bayani: Amirka za ta saka hannayen jari a Afirka
A shekara ta 2022 gwamnatin Biden da Harris ta sanar da wani tsari ga kasashen Kudu da Saharar Afirka tare da alkawarin dalar Amurka biliyan 55 yayin taron Amurka da shugabannin Afirka a 2022. Sai dai ba a kara adadin tallafi da Amurka ke kai wa Afirka ba, duk da cewa Biden na shirin kai ziyara kasashen Angola da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da kuma Zambiya.
Ita ma Harris ta yi alkawarin za ta tabbatar da ganin tasirin Amurka ya haura na Chaina a karni na 21, tare da yin kira kan shiga al'amuran Afirka sosai. Babban abin da ke gabanta ko kuma Trump in har sun lashe zaben dai, shi ne farfado da tsarin nan na AGOA da zai tallafa wa bunkasar Afirka da kuma samar da damammaki wanda ke shirin kawo karshe a shekara ta 2025 da ke tafe.