Ministan harkokin wajen Rasha na ziyara a Afirka
June 4, 2024Ministan harkokin wajen na Rasha Sergei Lavrov ya samu tarba daga takwaransa Guinea Conakry Morissanda Kouyate, daga bisani kuma ya gana da shugaban mulkin sojin kasar Mamady Doumbouya. Wannan ce ziyarar Lavrov ta farko a Guinea a cikin shekaru 11, tun bayan wadda ya kai a shekarar 2013.
Yayin taron manema labarai a Conakry, Mr Lavrov ya jaddada kudirin Rasha na ci gaba da yaukaka alaka ta fannoni da dama da Guinea da ma sauran kasashen Afirka kawayenta.
Karin Bayani: Shekaru biyun mulkin soja a Guinea Conakry
''Kamfanoninmu da ke aiki a Guinea na samun tagomashi matuka, sakamakon kyakkyawar shimfidar da kasar ke musu wajen ganin sun gudanar da ayyukansu cikin nasara. Muna fatan ganin wanzuwar wannan lamari cikin walwala da jin dadi''.
Wannan dai na zuwa ne bayan da dangantaka ta yi tsami tsakanin wasu kasashen Afirka da uwargijiyarsu Faransa da kuma Amurka, har ma suka yanke duk wata alaka da ke tsakaninsu. A daidai lokacin da juyin mulki ke zama tamkar wutar daji a kasashen yammacin Afirka.
Mr Lavrov ya ce alamu na nuna cewa tafiyar za ta yi nisa tsakanin Rasha da Afirka.
''Muna da kwarin gwiwar cewa harkokin cinikayya da kasuwanci za su kara bunkasa a cikin wannan kawance namu da Guinea, ko da yake an 'dan samu koma-baya a shekarar 2023 da ta gabata. Amma wannan ba zai sanyaya mana gwiwa ba, nan gaba za mu waiwayi fannin arzikin albarkatun karkashin kasa, da na ruwa irin su kifaye da kuma noma, sai bangaren makamashi, da nufin inganta su''.
Karin Bayani: Kawancen Afirka da Rasha na kara kankama
A taron manema labaran Sergei Lavrov bai gushe ba sai da ya tabo batun sake dawo da wata yerjejeniya da kasashen biyu suka cimma a baya ta huldar diflomasiyya.
''Ina fatan jaddada muku cewa mu'amalarmu ta tsakanin gwamnati da gwamnati na dab da dawowa nan ba da jimawa ba, don samun kyutatuwar hadin kai da huldar kasuwanci da cinikayya, wadda muka gaza cimmawa tun a shekarar 2019''.
Bayan kammala ziyarar Guinea Conakry, Mr Lavrov zai wuce zuwa Jamhuriyar Congo, inda zai gana da shugaba Denis Sassou N'Guesso, kamar yadda hukumomin Brazaville suka sanar.
Kasashen da Rasha ta kulla kyakkyawar alaka da su sun hada da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso, wadanda yanzu haka ke hannun sojoji bayan juyin mulki.