1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO na taro kan shirin tallafa wa Ukraine

April 4, 2024

Ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO na gudanar da taro a hedikwatar kawancen da ke birnin Brussells inda suke tattaunawa kan shirin tallafa wa Ukraine.

https://p.dw.com/p/4eQle
Ministocin NATO na tataunawa kan shirin tallafa wa Ukraine
Ministocin NATO na tataunawa kan shirin tallafa wa Ukraine Hoto: Geert Vanden Wijngaert/AP Photo/picture alliance

Wannan taro na zuwa ne a daura da bikin cika shekaru 75 da kafa kawancen tsaron wanda aka yanke wa cibiya a ranar hudu ga watan Aprilun 1949 bayan yakin duniya.

 Karin bayani: Shekaru 75 da kafa kungiyar tsaro ta NATO

A jajibirin taron, sakataren NATO Jens Stoltenberg ya bayyana damuwa kan raguwar hadin kai wajen tallafa wa dakarun Ukraine da ke fama da matsaloli a fagen daga da kuma gaza cimma matsaya kan shigar da Kiev cikin kungiyar tsaron da kawo yanzu ke da membobi 32.

Kazalika wasu minstocin kasashen da suka shiga kungiyar a baya-bayan nan sun bayyana yakin Rasha da Ukraine a matsayin yaki mafi girma ga kawancen, tare da bayyana fargaba kan dakatar da yiwuuwar katse tallafin da Washington ke bai wa Kiev muddin Donald Trump ya sake dawowa kan karagar mulkin Amurka.

Karin bayani: NATO na waiwaye kan cika shekaru 75 da kafuwa

A jajibirin wannan biki a cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kasashen Jamus da Faransa da Poland sun shawarci sauran kasashe membobin kungiyar da su ware kashi 2% kan harkokin tsaro duba karuwar barazana da Turai ke fuskanta daga Rasha.