1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 75 da kafa kungiyar tsaro ta NATO

Bernd Riegert, Sulaiman Babayo/Abdoulaye Mamane
April 4, 2024

Kungiyar tsaro tsaro ta NATO da aka kafa shekarar 1949 na bikin cika shekaru 75 da kafuwa a daidai lokacin da abokiyar gabarta Rasha ke tsaka da yaki da Ukraine.

https://p.dw.com/p/4eQN0
Kawancen kungiyar tsaro na NATO na bikin cika shekaru 75 da kafiwa
Kawancen kungiyar tsaro na NATO na bikin cika shekaru 75 da kafiwa Hoto: Stasonych/Pond5/IMAGO

An kafa kungiyar tsaro ta NATO/OTAN a ranar hudu ga watan Afrilun shekarar 1949, ta kasance yanzu kungiyar tsaro mafi dadewa da ta kumshi kasashen da suke bin tsarin dimukaradiyya.

A shekarar 1949 kungiyar kawancen tsaron ta fara da kasashe 12, daga baya ta samu karin kasashe 20 inda yanzu take da mambobi 32. Kasashen Finland da Sweden na zama na baya-baya da suka shiga kungiyar domin neman kariya daga Rasha.

Karin bayani : NATO na waiwaye kan cika shekaru 75 da kafuwa

Kasashen Ukraine da Georgia sun amince da shiga kungiyar shekaru 25 da suka gabata, bisa wannan dalilan aka fadada kungiyar NATO tare da shigar da wasu tsaffin mambobin kungiyar tsaron Warsaw, bayan rushewar kawancen na gabashin duniya, abinda ya haifar da kasashen Poland da Jamhuriyar Czech da Hangari shiga NATO.

Wasu shugabannin kasashen nahiyar Turai na murnar cika shekaru 75 da kafa kungiyar tsaro ta NATO
Wasu shugabannin kasashen nahiyar Turai na murnar cika shekaru 75 da kafa kungiyar tsaro ta NATOHoto: Kenzo Tribouillard/AFP/Getty Images

Matthias Dembinski na wata cibiyar kula da zaman lafiya da rikice-rikice a Jamus yana ganin har yanzu babu sauyi kan martani daga kungiyar tsaron NATO tun lokacin da aka kafa kungiyar

"Babban abinda ke gaban kasashen Turai mafi muni shi ne fuskantar abubuwa biyu. Kama daga cika burin mahukuntan siyasa na Amirka da kuma ba da gudumawar soja kamar yadda Amirka take yi zuwa yanzu."

Akwai lokacin da ita kanta Rasha ake mata ganin mai dasawa da kungiyar tsaron NATO inda ta zama mai wakilcin saka ido a shekarar 1997, yayin da NATO ta ci gaba da fadada, sai dai shugaba Joe Biden na Amirka ya ce matakin kungiyar na kare juna shi ne babban matakin kariya na kawancen.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden
Shugaban kasar Amurka Joe BidenHoto: Petras Malukas/AFP

"Yau kungiyar kawance tana ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro kamar yadda ta saba fiye da shekaru 70 da suka gabata. NATO ta kara karfafa cike da kuzari fiye da kowane lokaci a tarihi."

A shekarun 2000, Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya soki kungiyar NATO wajen fadada zuwa kusa da iyakar Rasha, inda ya yi ikirarin cewa bayan shigar da Jamus ta Gabas cikin kungiyar sakamakon hadewa da Jamus ta Yamma a shekarar 1990 an yi alkawarin dakile fadada kungiyar kawancen, sai dai babu inda aka yi haka ko a rubuce. Boris Pistorius ministan tsaron Jamus ya ce kawance yana da tasiri har yanzu.

Karin bayani : An daga turar Sweden a harabar shedikwatar NATO

"Muna juya komai cikin hanzari. Mana kokarin tsayar da rikici tsakanin kasa da kasa. Mun duba kawance tsaron tsakanin kasashe domin kariya. Haka na daukan lokaci. A inda muke ke nan muna kara duba bangarorin daban-daban, yadda nake ganin lamura ke nan."

Jamie Shea tsohon daraktan sadarwa na kungiyar ta NATO yana ganin sakamakon yakin Rasha da Ukraine zai tantance makomar kawancen, sai dai har yanzu wasu lokuta ana ganin mabanbantan ra'ayi kan batutuwa tsakanin bambobin kawancen.