Ministocin tsaron Turai za su gana gabanin rantsar da Trump
January 13, 2025Ministocin tsaron kasashen Poland da Jamus da Faransa da Italiya da kuma Burtaniya, za su gana nan gaba a ranar Litinin a birnin Warsaw domin tattauna batutuwan tsaro.
Ganawar mai manufofi biyar kan tsaron da aka assasa tun bayan lashe zaben Amurka da Donald Trump ya yi, na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake shirye-shiryen rantsar da sabon shugaban na Amurka.
Ministocin tsaron EU za su tattauna kan horas da sojin Ukraine
Kasashen na nahiyar Turai suna nema wa kawunansu mafita ne ganin yadda ake da rashin tabbas a kan Trump a kawancen NATO baya ga kokarin karfafa tsaro a nahiyar ta Turai.
Ya zuwa yanzu babu wanda ya san adadin tallafi da gwamnatin Trump za ta iya bai wa Ukraine a yakinta da Rasha mako daya kafin kafa gwamnatin.
Taron ministocin tsaron ƙungiyar EU a Portugal
Har ila yau, ministocin tsaron na nahiyar Turai za su tattauna kalaman Trump na neman kwace yankin Greenland da ke karkashin kasar Denmark da kuma kutse a kasar Canada.