Mutanen farko da aka kwashe daga Gaza sun isa Masar
November 1, 2023Rukunin farko na baki da 'yan kasashen waje sun isa Masar daga zirin Gaza wanda Isra'ila ke yi wa luguden wuta ba kakkautawa bayan da dakarunta suka kutsa dan karamin yankin ta kasa.
Karin bayani: Yakin Gaza ya hallaka mata da kanana yara kusan dubu shida
Wani baban jam'in Masar ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa rukunin farko na mutanen ya hadar da mata da kananan yara da kuma tsofaffi, kana kuma sun shiga kasar ne ta iyakar Rafah da ke zama kofa daya tilo da ke sada zirin Gaza da sauran sassan duniya.
Karin bayani: Rokoki sun jikkata mutane a iyakar Masar da Isra'ila
A kiyasin da aka bayar dai 'yan kasashen waje 44 ne da suka hada da ma'aikatan hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu 28 ke a makale a dan karamin yankin na Falasdinu mai al'umma miliyan 2.4.
Wannan dai shi ne karon farko da aka bai wa mutane damar barin zirin Gaza wanda dakarun Isra'ila suka yi wa kawanya cikin makonni.