Halin matsin rayuwa a Najeriya
September 3, 2020Kungiyoyin kwadagon Najeriyar dai sun bayyana cewa tura ta kai bango, yayin da gwamnatin kasar a nata bangaren ke fadin kasuwa na zaman alkali. Duk da cewar dai an dauki lokaci ana ji a jiki sakamakon annobar COVID-19 da tai barazana ga miliyoyin al'ummar Najeriyar, daga dukkan alamu sabon kari na farashin man fetur da kudin hasken wutar lantarki, na neman jawo sabon rikici a tsakanin ma'aikata da gwamnatin kasar.
Karin Bayani: Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin mai
Karin da ke zaman irinsa na hudu a tsawon wattani uku dai, daga dukkan alamu na neman yamutsa lamura a cikin Najeriyar, kasar da al'ummarta ke ji a jiki sakamakon hauhawar farashi na abinci da tsada ta rayuwa a cikin halin annoba. Abujar dai na a tsakanin ci gaba da cin bashin cikin gida da lamuni na kasashe na ketare, wajen iya sauke nauyin manya ayyuka da kuma biyan tallafi ga harkokin man fetur da wutar lantarkin tare da mantawa da batun na ayyukan raya kasa sakamakon annobar COVID-19.
Karin Bayani: Mafita kan matsalar tattalin arziki da tsadar rayuwa
Kasar dai ta tsara cin bashin d aya kai dalar Amurka Miliyan dubu22 da nufin iya sake gina ababe na more rayuwar al'umma da suka dauki lokaci suna lalace. To sai dai kuma karin da ko bayan man fetur da wutar ya kai har ga haraji na yan kasar dai daga dukkan alamu ya harzuka masu kodagon tarrayar Najeriya dake fadin tura ta kai bango an kuma kare hakurinsu.
Ayuba Wabba dai na zaman shugaban kungiyar kwadagon kasar ta NLC da kuma ya ce suna shirin kiran taron gaggawa da nufin nazarin yanayin da ke zaman ba sabun ba da kuma ke nuna irin jan aikin da ke gaban ma'aikatan da ke fafutuka ta rayuwa cikin albashi mara kyau.
Karin Bayani: Samar da lantarkin Najeriya a hannun 'yan kasuwa
Ya zuwa ranar yau dai tana kara fitowa fili cewar kudin hasken wutar lantarkin, ya ninka har sau uku a wurare irin babban birnin tarayya na Abuja, a yayin da farashin man fetur ya koma ya zuwa Naira 160 kan kowace lita. Abun kuma da ko bayan ma'aikatan ya bata ran dillallan man fetur da ke kallon raguwar jari sakamakon tashi na farashin a fadar Abubakar mai Gandi da ke zaman mataimakin shugaban kungiyar dillallan man masu zaman kansu ta kasar IPMAN. Jeri na matakan da ke nuna alkiblar gwamnatin na zare tallafin da ta saba a bisa bukatar makamashi ta 'yan kasar mai tasiri dai, na zuwa ne a lokacin da kasar ke fuskantar rashin aiki da matsalar tsaro, baya ga rawar da annobar COVID-19 ke takawa. Akalla kaso 27 cikin 100 na al'ummar Tarayyar Najeriyar ne dai ke zaman kashe wando, a yayin da shi kansa tattali na arzikin ya kalli tsukewa mafi girma a lokaci mai nisa sakamakon annobar.