Tsadar rayuwa ta yi muni a Najeriya
February 6, 2024Cikin tsawon watanni guda shida da zare tallafin man fetur dai jihohin cikin kasar sun samu akalla Naira tiriliyan uku a wani abun da ke zaman karin da ya kai kusan kaso 20 cikin dari na kudade na shiga na shekarar da ta shude. To sai dai kuma karin daga dukka na alamu ya gaza sauya rayuwar al’ummar tarrayar Najeriya da sannu a hankali ke neman komawa ya zuwa zanga-zanga. Zanga-zanar kuma da ke neman rikidewa zuwa gaba ta siyasa inda jam’iyyar APCmai mulki ke zargin adawar cikin kasar da neman tunzura al’umma a tituna. Wata sanarwar hedikwatar jam’iyyar ta kasa dai ta ce zanga-zangar Kano da birni na Mina dai na da kafa da kila ma hannayen jam’iyyu na adawa. Zargin kuma da a cewar matamaki na kakakin PDP ta adawar Ibrahim Abdullahi ke kama da gazawar ‘yan mulkin da ke ta kara fitowa fili.
Duk da alkawarin da gwamnatin Najeriya ta yi wa al'umma rayuwa ta yi tsanani
‘
Cikin alkawarin 'yan mulki dai zare tallafin zai kaiwa ya zuwa karin kudin shigar raya kasa da kila sauya makomar al’umma, bayan share shekara da shekaru ana zargin tallafin da komawa sanadi na talauci cikin kasar. To sai dai kuma rashin gani cikin kasa watanni shida bayan zare tallafin a tunanin Dr Isa Abdullahi da ke zaman kwarare bisa tattali na arzikin na zaman ummul aba’isin, neman tada hankali na 'yan kasar a halin yanzu.Tun ba’a kai ga ko’ina a shekarar 'yan kasar na kallon farashi na abinci da bukatu na rayuwar yau da ta gobe na neman ya wuce da tunani na mafi yawa na 'yan kasar a halin yanzu.