Najeriya za ta kara wa ma'aikata albashi
January 29, 2024Karin albashin ma'aikata na karshe da Najeriyar ta yi shi ne shekaru shida da suka wuce, inda ta sanya mafi karancin albashin zuwa Naira 30,000
Sai dai kuma zare tallafin man fetur da daidaito bisa farashin dala ya sake tada tsohon miki a tsakanin ma'aikatan kasar da ke fadin tayi baki da kuma masu mulkin tarrayar da ke tunanin mafita.
Ya zuwa yanzun dai kungiyar kodagon tarayyyar Najeriyar NLC na neman akalla Naira 200,000 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata a kasar. Kuma a ranar Talata ce Abujar ke kaddamar da wani kwamiti na bangarori da yawa da nuifn nazarin bukatar ta kodago dama tunanin mafita cikin kasar da ke fadin ba dadi.
Karin Bayani:Najeriya: Rikicin karin albashi ga ma'aikatan tarayya
Jihohi da yawa dai sun gaza kaiwa ga biyan 30,000 yanzu sakamakon korafin rashin kudin tafiyar da harkokinsu. A yayin kuma da damansu ke zuwa cin bashi da nufin sauke nauyin da ya maida jihohin cibiyar biyan albashi maimakon kafa ta cigaban al'umma.
Masu kodagon kasar dai na yiwa karin albashin kallon damar rage talauci a kasar da hauhawar farashi ke neman wuce tunan mafi yawan yan aikin.
Najeriyar dai na zaman ta kurar baya a nahiyar Africa wajen albashin a fadar Dr isa Abdullahi kwararren masanin tattalin arziki.
Karin Bayani:Takaddama kan karin albashi a Najeriya
Tuni dai batun karin albashin ya fara jawo tada hakarkari a kasar a halin yanzu. Akwai dai tsoron karin na iya kara jefa daukacin al'ummar kasar da ke fadin ta yi baki zuwa baki kirin sakamakon hauhawar farashin bukatun rayuwar yau da ta gobe.
Duk da cewar ana shirin tattaunawa daga yanzu, sai a watan Aprilun da ke tafe ne dai ake sa ran sabon mafi karancin albashin ya fara shiga aljihun ma'aikata bisa alkawarin yan mulkin. Kundin tsarin mulkin kasar dai ya tanadi muhawara da ma amincewar majalisar dokoki kafin iya kaiwa ga fara aiwatar da duk wani karin albashin ma'aikata a kasar.