1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba barazanar matsalar abinci a Najeriya

September 10, 2020

Kasa da tsawon makonni biyu da wata ambaliyar ruwa da ta lalata kusan kaso 25 cikin dari na daukacin shinkafar da kasar ta noma a shekarar bana, Najeriya ta ce babu damuwa game da barazanar yunwar da ake fuskanta.

https://p.dw.com/p/3iIYA
Symbolbild I Nigeria I Islamisten nehmen Geiseln
Matsin rayuwa da yunwa sakamakon tsadar abinci da kayan masarufi a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Kusan tan miliyan biyu na shinkafa ne dai kasar ta kai ga asara, sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye sassa daban-daban na Tarayyar Najeriyar makonni biyu baya.  Da ma dai tuni  matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa maso Yammaci da ma Tsakiyar kasar, ya yi barazana ga noman masara da ita kanta shinkafar, a wani abun da ke zaman koma baya ga kokarin kasar na wadatar da kai da abinci.

Barazanar karancin abinci karancin na abinci game da karuwa ta bukata dama kila al'adar a saya a ajiye a bangare na masu kasuwar kasar dai, ya tsawwala farashin abinci zuwa kololuwar da babu irinta a daukacin tarihin Najeriyar. To sai dai kuma gwamnatin kasar ta ce tana daukar matakai da nufin kaucewa yunwar da ke iya zamowa sabuwar barazana ko bayan fatarar da ke ta karuwa cikin kasar a halin yanzu. 

Karin Bayani: Najeriya: 'Yunwa ta fusata 'yan gudun hijira 

Kafin tsarin tsadar dai batun na abinci na zaman na kan gaba da 'yan kasar ke samu a cikin sauki, sakamakon share kusan shekaru biyu ba tare da kallo na tashintashin farashin na cimaka a kasar ba.

Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

An dai kare wani taron majalisar samar da abinci a Najeriyar, inda gwamnatin kasar ta ce tana daukar jeri na matakai da nufin kare sana'ar noman da kuma tabbatar da inganta wadatar ta abinci, a cewar shugaban kasar Muhammad Buhari. "Domin kare jarin da ke cikin harkar noma, mun saka dubban sojojin kare gonaki  da kuma hade kauyuka da tattali na arziki ta kara hanyoyi a karkara. Mun zuba jari wajen gina rumbunan ajiyar rarar abinci, kamar bashi da bukatun noma ga maanoman kauye. Kuma a kwanan nan mun samar da  abinci ga talakawa da kamfanonin da basu da karfi domin rage radadin COVID-19. To sai dai kuma abun takaici, ambaliyar ruwan kwanan nan ta shafi tsare-tsaren da muka yi, an yi asarar rai kuma an yi asara ta dukiya. Ina mika jajena ga asarar rai da dukiyar da ta faru sakamakon ambaliyar. A gwamnatance, za mu yi iyakaci na iyawa wajen tallafawa wadanda asarar ta rutsa da su. Tuni dai mun fara kokarin ganin mun mai da asarar da muka yi a damina a cikin noman rani na gaba."

Karin Bayani: Azumi cikin yanayin kunci da fargaba a Najeriya 

To sai dai koma ta ina kasar take shiruin bi da nufin rage radadi da kila ma sauke farashi na abincin dai, daga dukkan alamu har yanzu da sauran fata a bangaren 'yan mulki na kasar na sake daidaiton lamura a kan hanyar wadata kai da abincin da ke iya rage zafin da 'yan kasar ke ji a ajiki. Atiku Bagudu dai na zaman gwamnan Kebbi kuma mataimakin shugaban majalisar abincin Najeriyar da ya ce kasar tai nisa  a kokari na kara yawan noman da take a cikin ranin da ke tafe domi rage tasiri na rashin abincin.