1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Bashi ya yi wa gwamnatin Najeriya katutu

March 18, 2022

A wani abun da ke zaman alamun komawa zuwa tsoho na karatun bashi, hukumar kula da bashin tarrayar Najeriya ta ce yawan bashin da ke kan kasar ya kai kusan Naira Trilliyan 39.

https://p.dw.com/p/48hml
Najeriya: Takardun kudin Naira
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A cikin wannan mako ne ma'aikatar kudi a tarrayar Najeriya ta ce ta samo wani sabon bashi na Dalar Amirka Miliyan dubu daya da kwata da nufin ci gaba a kokarin samar da abaen more rayuwa. Bashin kuma da ya dauki kasar zuwa wani sabon matsayi a cikin karatun bashin kuma ke kara tada hankali 'yan kasar inda a bara kadai dai Najeriya ta ci bashin da ya haura Trilliyan shida adadin kuma da ya kai kusan rabin kasafin kudin kasar na shekarar da ta shuden.

Sannu a hankali Najeriya na neman komawa zuwa karatun baya, inda bashi ya zamo tarnaki ga harkar mulki ya kuma tsayar da kokarin raya kasar kafin wata afuwa a shekarar 2006 da kungiyoyin bashin kasashen Yamma suka yi na kusan dalar Amirka Miliyan dubu 32. Ya zuwa yanzu bashin da ke kan gwamnatin tarrayar da jihohi ya sake haurawa tare da kaiwa Naira Trilliyan 39, ko kuma Dalar Amirka Miliyan dubu 95, adadi mafi yawa a daukacin tarihi na kasar. Gwamnatin Najeriya na fadin zabi ko na cin bashin da nufin aiwatar da muhimman aiyyuka a cikin kasar, ko kuma mantawa da babban buri na ci gaban al'umma.

Karin bayani: Buhari zai sake ciyo bashi ga Najeriya

Shugaba Buhari da Sanata Ahmad Lawal da Femi Gbajabiamila
Shugaba Muhammadu Buhari da Sanata Ahmad Lawal da Femi GbajabiamilaHoto: Nigeria Prasidential Villa

Senata Ahmed Lawal shugaban majalisar dattawa ta kasa ya ce tarrayar Najeriya na tsaka a talauci duk da karuwar farashin man fetur a duniya baki daya. "Yayin da abu ya zama tilas ba yadda za ka yi. Duk yadda kake so kar ka dauki bashi a matsayinmu na kasar Najeriya to sai mu duba ta ya za mu samu kudin ginin ababen raya kasa irinsu tituna da gadoji da ke kan tituna da bunkasa tattalin arziki? Gaskiyar magana ita ce Najeriya ba ta da kudi, Najeriya na cikin rashi, Najeriya na cikin talauci, kudin da muke samu daga harkar man fetur bai kai kaso 25 cikin dari na bukatarmu ba."

Karin Bayani:  Fargabar matsalar tattalin arziki a Najeriya

A yanzu tarrayar Najeriyar kaso 97 cikin dari na kudadenta na shiga wajen biyan ruwan bashi da ya kai kusan Trilliyan Uku a shekara. Abubakar Aliyu masanin tattali arziki na cewa hakan na da babbar ila ga makomar Najeriya.

Ya ce: "Lafiya muna nema a waje, makarantu muna nema a waje, man fetur muna nema a waje, kusan komai muna tafiya yana kara zubewa. Kowa yazo abi yarima asha kida a tafi. To ba zai yiwu ba, don kasar ba za ta dauki barnar da ake mata ba, saboda za ta tsaya cak, kuma in ba a yi hankali ba hakan zai zo na ba da jimawa ba. Ya kamata a yi ribas a duba aga yadda za a ceci kasar nan. A dau bashi ayi almubazzaranci, a dau bashi a yi cin hanci da rashawa, a dau bashi a ba da kwangilar miliyan dari ko biliyan biyu, to in ba a yi hankali ba bashin zai tsaya a wuyan kowa."

Hoton barkwanci: Sayar da kamfanonin gwamnati
Hoton barkwanci kan tattalin arzikin NajeriyaHoto: Abdulkareem Baba Aminu

Karin bayani: Majalisa ta ki yarda da bashin sayen gidan sauro

Ko bayan aiyyuka na raya kasa dai tashin farashin makamashi na son ba wa tarrayar Najeriyar neman wani bashi na dalar Amirka Miliyan dubu biyu da nufin shigo da hajjar man fetur a Najeriya da ke neman lamushe Triliyan kusan Hudu ta Naira.