1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bude makarantu bayan hutun kullen Corona

Abdullahi Maidawa Kurgwi
January 18, 2021

A Najeriya an bude makarantu a fadin kasar bayan tsawon lokaci da makarantun suka kasance a rufe sakamakon yaduwar cutar Coronavirus. 

https://p.dw.com/p/3o5fG
Nigeria Studenten in Jos
Hoto: picture-alliance/epa/Ruth McDowall

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da bude makarantun gwamnati da masu zaman kansu, makarantun suka soma shirin karatu yadda aka tsara tare da bin ka'idoji na matakan kariyar cutar Corona na bada tazara da sanya abin rufe baki da hanci da kuma amfani da sinadarin wanke hannu kamar yadda gwamnati ta shimfida.

Kodayake wasu rahotanni sun ruwaito wani bangaren majalisar wakilan Najeriya na cewar bai kamata gwamnatin kasar ta bari a bude  makarantun ba har sai bayan watanni uku nan gaba don gudun yada cutar Coronavirus, to amma wasu iyaye na ganin cewar kamata yayi gwamnati ta bari daliban su cigaba da karatu, illa kawai a dauki matakan kariya a makarantun.

Jami’an ma’aikatar ilimi a jihar Filato sun shaida wa wakilin mu Abdullahi Maidawa Kurgwi cewar za su rika kai ziyara makarantu akai akai don tabbatar da ganin suna bi ka’adojin yaki da cutar covid-19, kuma duk makarantar da ta karya ka’dodjin yaki da cutar za a rufe ta nan take . 

Akasarin makarantun gwamnati da na jama’a masu zaman kansu dai ciki harda jami'oi sun kasance a bude a wannan rana, yanzu abin jira a gani shi ne ci gaban karatun har zuwa karshen zangon karantun kamar yadda aka tsara.