Harajin yaki da zambar Internet a Najeriya
May 7, 2024Za a yi amfani da kudin harajin da aka dauka a asusun ajiyarsu na bankin ne, wajen gudanar da cibiyar yaki da laifuffukan da ake aikatawa ta kafar Internet din da suka bata sunan Najeriyar. Babban Bankin Najeriyar CBN ne ya bayar da umurni ga bankuna su fara cire karin digo biyar na duk kudin da masu ajiya suka aika ta asusunsu, a matsayin wannan haraji na yaki da laifuffukan da ake aikatawa ta Internet a cikin kasar da a kullum ke kara fadada. Kama daga masu zambar kudi ta Internet ya zuwa masu satar bayanai da masu safarar dan Adam da sayar da miyagun kwayoyi, duk sun koma a dandalin sada zumunta suke aikata wadannan laifuffuka. Wannan haraji dai ya samu zama halastace ne a Najeriyar, bayan kafa dokar yaki da laifuffukan da ake aikatawa ta Internet a cikin kasar a 2015 da ta samar da hakan.
Sanin cewa akwai dimbin masu karamin karfi da ke ajiya a bankin domin bukatarasu ta yau da kullum kuma suke ciki matsai na rayuwa, wacce matakin zai ba su? Mallam Yusha'u Aliyu masani a fannin tattalin arziki da ke Abuja, ya ce akwai bukatar taka tsan-tsan a kan lamarin. Bankunan Najeriyar dai sun kasance kan gaba wajen tafka mummunar asara a dalilin laifuffukan zamba cikin aminci ta kafar Internet din, lamarin da ke zubara da mutuncin kasar a idanun duniya. Koda yake gwamnati ta bayyana aniyarta ta tabbatara da tsarin ya tafi daidai wajen yaki da masu wannan mumunan dabi'a, amma Dakta Kabiru Adamu masani kan harkokin tsaro a kasar na ganin akwai sauran gyra a kan lamarin. Yaki da masu aikata wadannan laifuffuka ta kafar Internet dai, lamari ne da kwararru suka bayyana cewa akwai bukatar kara azama.