Zaman dirshan na 'yan awaren IPOB
May 28, 2021'Yan kungiyar ta Biafra bangaren IPOB din dai, sun ce za su yi zaman dirshan din ranar Litinin din a gidajensu, kuma sun ce a ranar ba batun zirga-zirgar jama'a ko ta ababen hawa a daukacin yankin Igbo. Tuni dai da daman makarantu suka sanar da rufewa, sannan mutane da dama na shiga kasuwanni domin tanadar ababen bukata na wasu kwanaki, sakamakon yanayin rashin tabbas da suke ganin za a shiga a yankin.
Ana dai zargin haramtacciyar kungiyar ta IPOB mai rajin Biafra da kai hare-hare kan jami'an tsaro da ofisoshinsu a yankin da ma a Niger Delta, wadda hakan ke dada dagula al'ammuran tsaro. Sanarwar da kungiyar ta yi na shirin zaman dirshan din a gidajensu tare da hana zirga-zirga a daukacin yankin Igbo, ta dada haifar da rudani.
Karin Bayani: Kama masu rajin kafa kasar Biafra a Najeriya
Kungiyar dai ta ce za ta yi amfani da ranar domin tuna 'yan mazan jiyansu da kuma tuna yakin Biafra da ya gudana shekaru 54 da suka gabata, inda duka kasuwanni tashoshin mota da makarantu da filayen jiragen sama, za su kasance a rufe a daukacin yankin mai jihohi biyar. A wani jawabin baya-bayan nan dai, jagoran kungiyar ta IPOB haramtacciya Mr Nnamdi Kanu ya kara kira ga 'yan yankin da su martaba wannan rana, tare da tabbatar da cewa komai ya tsaya cik.