INEC na da jan aiki kafin zaben Najeriya
January 4, 2023Sama da mutane miliyan 100 ne dai suka yi rijista, domin taka rawa a cikin zabukan da ke shiri su gudana a watan gobe. To sai dai kuma sabuwar barazana na neman kunno kai ga batun zaben, inda miliyoyin 'yan kasar ke ko oho a kokarin karbar katin zaben. Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasar INEC ta ce sama da katuna miliyan shida da rabi ne ba a karba ba, kasa da makonni uku da kamalla aikin karbar katin. Tun a watan Disambar shekarar da ta gabata ne dai, aka fara aikin karbar katin bayan wani dogon lokaci ana kace-nace kan rijistar masu kada kuri'ar. Kama daga share tsawon kwanaki a ofisoshin INEC da nufin samun katin ya zuwa kokarin sayen kati a bangaren masu siyasar da ma uwa uba dawowa daga rakiyar masu taka rawa a mulkin kasar, batutuwa da daman gaske ne dai ake yi wa kallon zaman kan gaba wajen dawowa daga kokarin taka rawa cikin shirin mai tasiri.
Iya yin adalci ko kuma kokarin sanyaya gwiwa dai, katin zaben na zaman hanya daya tilo a kokarin kai wa ya zuwa babban aikin samar da ingantattun shugabanni a kasar. Kuma afadar Sha'aban Sharada da ke zaman dan takarar gwamna a jihar Kano, samun katin a karkashin sabon tsari BVA na zamani na iya kai wa ya zuwa sauya da dama da kila ma ceto 'yan kasar da ke ta wayyo Allah yanzu. Kokarin kwatar 'yanci ko kuma mika wuya zuwa ga hallaka dai, a ranar 22 ga watan nan ne aka tsara kamalla karbar katin zaben. Kuma INEC din a fadar kakakinta Zainab Aminu na shirin sauya da dama da nufin kai katin kowane sako cikin kasar a nan gaba. A jihohi da dama dai, hukumar ta INEC din na da jan aikin sake buga sababbin katunan, bayan kona ofisoshi da kaddarorin hukumar a sassa dabam-dabam na kudanci na kasar.