1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen babban zaben Najeriya na 2023

Uwais Abubakar Idris SB
February 14, 2023

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Najeriya INEC, ta sanar da cewar ba za a gudanar da zabe a rumfuna 240 da ke jihohi 28 na kasar ba.

https://p.dw.com/p/4NTtc
Najeriya | Zabe l INEC
Ba a za yi zabe a rumfuna sama da 200 a NAjeriyaHoto: Stefan Heunis/AFP

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriyar INEC, ta dauki wannan matakin ne bayan da masu kada kuri'a suka ki amincewa da su yi zabe a wurarren da mafi yawansu sababbin runfuna ne da aka kirkiro saboda matsaloli na rashin tsaro. Wannan dai na zuwa ne kasa da makonni biyu kafin a gudanar da babban zaben na Najeriyar, kana bayan da hukumar ta INEC ta kara rumfunan zaben da ake da su a Najeriyar bayan shekaru 25. Koda yake zabi ne da masu jefa kuri'ar bisa radin kansu suka nuna basa son zuwa wadannan runfuna domin kada kuri'unsu zabubbukan da za a yi a ranakun 25 ga wannan wata Fabarairu da muke ciki da kuma 11 ga watan Maris mai zuwa, sai dai ganin jihar Imo ta kasance kan gaba cikin jihohin da abin ya shafa ya sanya nuna batu na rashin tsaro da yadda zai iya shafar zaben kansa.

Najeriya | Zabe | INEC | 2023
Mata da matasa masu yawa, sun yi rijistar zaben da ke tafe a NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Rashin tsaron dai ya sanya samar da rumfunan zabe kusa da jama'a, maimakon sai sun yi doguwar tafiya. Wannan ya nuna za a samu raguwar mazabun da za a yi amfani da su a wannan zabe daga sama da runfuna zabe dubu 176 da 846 a yanzu, zuwa rumfuna dubu 176 da 606. To sai dai fitattun 'yan siyasu kamar Isa Tafida Mafindi na da ra'ayin cewa, babban abin bukata shi ne fitowar jama'a kuma a yi zaben cikin kwanciyar hankali. Ana fatan samun sauyi a zaben na wannan shekara a Najeriya, musamman yadda matasa da mata da yawa suka yi rijista wadanda ke kara jajaircewa kan cewa za su tabbatar da ganin zaben nasu ya yi tasiri, abin da zai iya sauya rashin fitowa zabe daga wannan jinsi da aka dade ana gani a Najeriyar.