Najeriya: Karancin man fetur na kara tsanani
April 30, 2024An dai dauki matakin nuna wa juna ‘yar yatsa a kan wannan matsala ta karancin man fetur din da ke kara yín kamari a kusan daukacin birane da kauyyukan Najeriya, inda matsalar ta jefa jama'a cikin mawuyacin halin. Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriyar ta bayyana cewa kodayake akwai karancin man amma dumbin bashin da suke bi na Naira bilyan 200 ya kara tazarar lamarin a cewar Alhaji Sirajo Kamba Yahya Kamba shugaban masu wuraren adana main a kungiyar ta Najeriya.
Karin Bayani: Karancin fetur ya kunno kai a Najeriya
Wakilin mu Uwais Abubakar Idris ya zaga zagaya wasu sassan Abuja inda ya tarar da dogayen layukan motoci a gidajen mai wanda ke nuna tsananta wahalar man fetur din. Tuni dai yan bumburutu suka sake bayyana saboda karancin man a Abuja bayan ban kwana da aka yi da sun a tsawon lokaci.
Karin Bayani: Karancin man fetur a Najeriya
Kamfanin man fetur na Najeriyar NNPC ya dage cewa akwai wadataccen mai domin 'yar matsala ce kawai aka samu kuma an shawo kanta.
Karin Bayani: Najeriya: Fata kan matatar man Dangote
Najeriyar dai duk da wadatar man fetir da take da shi har yanzu ta kasa magance matsalar karancin man da ake fuskanta daga lokaci zuwa lokaci duk da janye tallafin da ta yi, da kuma ikirarin mika daukacin harakar ga hannun 'yan kasuwa.