Yankin arewacin Najeriya ya fi yawan matalauta
November 18, 2022Rahoton da Hukumar kula da kididdigar kasar ta fitar, ya nuna cewa mutane miliyan 133 ne ke rayuwa a hali na talauci a kasar saboda matsaloli na koma bayan tattalin arziki da kuma rashin tsaro.
Rahoto da aka yi bincike mai zurfi a kan hali na zamantakewar rayuwa da ‘yan Najeriyar ke ciki, ya gano cewa kashi 65 na al'ummar kasar sun afka cikin hali na ukubar talauci. Kashi 65 cikin dari na wadanda ke fama da talauci suna a yankin arewacin Najeriyar ne, watau mutane milyan tamanin da shida a yayin da kashi talatin da biyar cikin dari na ‘yan Najeriyar da ke fama da talauci suke a yankin kudancin kasar.
Karin Bayani: Darajar Naira na kara faduwa a Najeriya
Jihar Ondo ce take da karancin matalauta a Najeriya da suka kai kashi asirin da bakwai a yayin da jihar Sokoto ke da kashi kashi casa'in da daya, abin da ya sanya ta zama kan gaba a yawan matalauta a Najeriyar. Lamarin da ya daga hankali shi ne gano cewa, kashi 72 in aka kwatanta da mutanen da ke rayuwa cikin talauci a birane da suka kai kasha 42.
Ana dai nuna ‘yar yatsa a kan gwamnatin Najeriyar a gaza samar da ci gaba ga al'umma musamman sanin ikirarin da take yi na raba mutane milyan dari da talauci.
Karin Bayani: Talauci na kara fadada a Najeriya
Bisa abubuwa da aka gano ya nuna da sauran jan aiki ga mahukuntan Najeriyar a batun ragewa al'umma talauci, domin rabon da a gudanar da irin wannan bincike tun a shekarar 2010, abin da ya sanya zuwa ido a ga ko zai sanya mahukunta su canza yadda suke tafiyar da al'ammuransu.