1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kera makamai na cikin gida a Najeriya don cike gibi

October 12, 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci ma’aikatar tsaron kasar da ta fara sarrafa makamai na cikin gida domin cike gurbin abin da za a iya nema na makamai a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalolin tsaro.

https://p.dw.com/p/41apw
Russland Waffe Kalaschnikow-Modell AK-47
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da haramtattun makamai ke kara yawaita a hannun wadanda ba su da amincewar hukumomi, abin da ake ganin ya sa harkokin tsaro na kara tabarbarewa.

Manufar ba da umurnin ga ma'aikatar tsaro da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da ta fara kera makamai na cikin gida shi ne rage dogaro da kasashen waje wajen samun makamai da sauran kayan yaki da Najeriya ke amfani da su wajen tabbatar da tsaron kasarta.

Wannan na nuna ke nan in har an bi umurnin na shugaban kasa kamfanin sarrafa makamai wanda ke karkashin ma'aikatar tsaro ta Najeriya za ta ke samar da isassun makamai wanda ba sai an je kasashen waje an sayo su ba.

Kungiyoyin 'yan takife da 'yan ta'adda a Najeriya sun mallaki manya-manyan makamai
Kungiyoyin 'yan takife da 'yan ta'adda a Najeriya sun mallaki manya-manyan makamai Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

To sai ba da wannan umurni na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da yaduwar haramtattun makamai a hannun mutane wanda aka yi kiyasin sun wuce yawan wadanda gwamnati ta mallaka wanda kuma har ya zuwa yanzu aka kasa raba mutane da su ko ma toshe hanyoyin shigar su a hannun mutane. 

Wannan mataki ya zo a wannan lokaci da matsalolin tsaro suka yi katutu a dukkanin sassan Najeriya. Yayin kuma da ake fargabar irin wadannan makamai za su iya fadawa hannun ba ta gari.

To sai dai masharhanta na ganin da wuya kasar ta iya samar da makamai na zamani da za a iya amfani da su wajen fuskantar matsalolin tsaro ganin yadda 'yan ta'adda da sauran masu gwagwarmaya da makami ke amfani da manyan makamai na zamani da yanzu ma suka gagari jami'an tsaron Najeriya a wasu wurare.

Amma wasu daga cikin ga talakawan kasar murna suka yi da wannan mataki saboda a cewarsu ko ba komai Najeriya za ta karu har ma wasu kasashe za su iya zuwa sayen irin wadannan makamai daga wajenta.