1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyara kan harkar man fetur a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
June 28, 2021

A Najeriya 'yan majalisar tarayya da suka fito daga yankin arewacin kasar, sun kammala wani taro a Abuja a kan kudurin dokar nan ta gyara fasalin harkar man fetur.

https://p.dw.com/p/3viGL
Öl Industrie
Najeriya dai na hako man fetur dinta daga yankin kudancin kasarHoto: public domain

'Yan majalisar tarayya na Najeriyar dai sun cimma matsaya a kan shirin da ake na amincewa da kudirin dokar sake fasalin harkar man fetur din da ma bukatun da suke da shi ga nasu yankin. Sun kwashe lokaci mai tsawo suna tattaunawa domin samun maslaha da ma sauki wajen amince wa da dokar Najeriyar da har yanzu yake tsole idanun kusan daukacin sassan kasar.

Karin Bayani: Matatun mai masu zaman kansu a Najeriya

'Yan majalisar wakilan da suka fito daga yankin arewacin Najeriyar a wannan karon sun sauya yanayin rawar da suka dade suna takawa, inda suka bayyana alkawarinsu na goyon bayan wannan kudurin doka saboda amfanin da suka ce sun hango a tattare da ita, kuma ma a wannan karon babu wata rufa-rufa da aka yi musu.

Ölgewinnung in Afrika - Symbolbild
Karancin matatun man fetur a Najeriya, na taimaka wa wajen samun karancinsaHoto: picture-alliance/A. Holt

Jihohin da suka fito daga yankin kudancin Najeriyar  inda ake hako albarakatun man fetir din kasar, sun nuna lailai da sake a yadda ake tafiyar da arzikin man fetur din da ya fito daga yankinsu, abin da a lokutan baya ya sanya kudurin dokar fuskantar jinkiri. To sai dai a wannan karon 'yan majalisar na yankin arewacin Najeriya, sun ce bukatarsu a tabbatar da samar da kudin binciken duk inda ake sa ran akwai man fetir a arewacin kasar. 

Karin Bayani: Rudani a kan karin farashin man fetur a Najeriya

Batun bude kafa ta zuba jari a harkar man fetri din Najeriyar dai muhimmi ne ga kudurin dokar a yadda aka tsarata a yanzu, abin da ya sanya bangaren majalisar da na zartaswa suka tattauna kan batun domin bunkasa harkar man fetur da iskar gas a Najeriyar. Tun a sherara ta 2008 ne aka fara gabatar da kudurin dokar, amma shekaru 13 har yanzu ana ja-in-ja a kanta. Abin jira a gani shi ne, ko a wannan karon majalisar za ta cika alkawari ta bai wa mara da kunya wajen amincewa da kudurin dokar ta sake fasalin man fetir din a Najeriya.