Daga man fetur zuwa ga iskar gas don gina arzikin kasa
March 29, 2021Duk da cewar hankali na dada karkata zuwa makamashi maras illa ga muhalli a duniya baki daya, ga tarrayar Najeriya iskar gas na shirin zama ta kan gaba ga tunanin 'yan mulkin da ke fatan gina tattali na arziki ko bayan alkinta muhalli.
Kuma mahukunta na kasar ba su biye ba wajen dora danbar karkatar kasar ya zuwa iskar da gwamnatin ke fatan na iya sauya da dama ga batun na tattalin arziki da zamantakewar al'umma.
Da ranar wannan Litinin dai Abujar ta kaddamar da sabon tsari na shekaru 10 da ke tafe da a cikin hankali zai koma ya zuwa iskar gas din domin kudin shiga da habbaka harkoki na tattali na arzikin kasar a nan gaba.
Karin bayani: Rudani a kan karin farashin man fetur a Najeriya
Ya zuwa wannan ranar dai kuma a fada ta gwamnatin kasar iskar gas din ta bai wa kasar abin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu 114 daga cinikinsa da sauran kasashe na duniya da ma bukatar cikin gida, adadin kuma da ke neman haura na man fetur din da farashinsa ke tashi da faduwa.
Kuma a fada ta shugaban kasar hankali 'yan mulki zai koma iskar gas din a kaco kam a nan da shekaru 10 da ke tafe.
"Abu ne da kowa ya sani Najeriya kasar iskar gas ce, mai man fetur na kalilan. Amma kuma abin mamaki kasar ta fi mayar da hankali ga harkar man fetur a lokaci mai nisa, wannan matsala ce muke son tunkara kai a tsaye da muka ayyana shekara ta 2021 zuwa ta 2030 a matsayin shekarun iskar gas a Najeriya. Babban sako ne domin tabbatar da shirinmu na cewar samar da iskar gas da amfani da ita zai dada samun fifiko a kasa, domin inganta tattalin arziki, kara samar da makamashi cikin kasa, habbaka jari da kuma samar da kari na ayyukan yi ga al'umma na kasarmu."
Karin bayani: Kotu ta gano masu satar fetur din Najeriya
Tarrayar Najeriya dai na da abin da ya kai kafa Triliyan 600 na iskar ta gas da ya mai da ita kasa ta tara a yawan iskar gas a duniya baki daya.
To sai dai kuma mafi yawa na iskar na konewa tare da lalata muhalli na kasar, ko kuma a cikin ramunkan hakar man fetur. Abin da Abujar ke neman sauyawa tare da karkatar da ita ya zuwa amfanin cikin kasar da ma a wajenta.
Timipre Sylva na zaman karamin ministan man fetur na kasar da kuma ya ce kasar ta farka bayan daukar lokaci cikin dogon bacci.
"Ina farin ciki da muke karkatar da tunani na kasar daga man fetur ya zuwa iskar gas, abin da muka gagara yi can baya. A nan ne muke iya gano karfi na tattali na arzikin kasarmu. Mu yi tunanin inda za mu iya samar da wutar lantarki daga iskar gas, ko kuma taki daga iskar gas din ko kuma sanadarin kimiyya da fasaha daga gas da za mu ga irin tasirinsa ga tattali na arziki, da kuma ayyukan da za a samar a kasa. In har muna tunanin fadada tattali na arzikinmu, to babbar hanya daya tilo ita ce iskar gas."
Ya zuwa yanzu dai kasar na gina wani bututu na dakon iskar gas mai tsawon kilomita 614 daga Ajakuta zuwa Kano. Ko bayan wani kamfani na hadin gwiwa a tsakanin tarrayar Najeriya da Moroco domin yin taki na zamani daga iskar gas din, da kasar ta sanar a makon da ya gabata.
Ko a cikin gida ma dai 'yan mulkin na dada habbaka amfanin gas din ko dai don girki, ko kuma motoci na hawa, abin kuma da a cewar Mele Kyari da ke zaman shugaban kamfanin mai na kasar NNPC ke iya sauya da dama ga rayuwar al'umma a nan gaba.