Makomar hada-hadar kudi a Najeriya
February 15, 2023Karin jihohin kasar 11 ne dai ya zuwa yanzu, su kai nasarar cusa kai cikin karar da tun da farko wasu jihohi uku suka kai babban bankin kasar da ita kanta gwamnatin tarayya. To sai dai kuma kotun da ta sake dage ssauraron shari'ar har ya zuwa Larabar makon gobe dai, ta ce a ci gaba da mutunta umarnin da ta bayar na tsayawa wuri guda dangane da batun amfani da tsofaffin takardun kudin Naira na kasar da aka sauya launinsu. Umarnin kuma da ya zuwa yanzu ke samun fassara dabam-dabam daga bakin lauyoyin kasar, kana yake kara fitowa fili a cikin sabon rudanin da ya mamaye miliyoyin 'yan kasar da har yanzu ke mallakar tsohon kudin amma kuma ke neman komawa zuwa asara babba. Tuni dai babban bankin kasar CBN ya sa kafa ya rushe umarnin, tare da tsayar da karbar tsofaffin kudin duk da umarnin da wasu lauyoyin ke fadin yana nufin ci gaba da tsohon tsarin.
Barrister Abdullahi Adamu Fage dai na zaman daya a cikin lauyoyin da ke wakiltar jihar Kano a zauren shari'ar, kuma ya ce sun shaidawa kotun kin bin umarnin da suke zargin babban bankin da ita kanta gwamnatin tarraya da yi. Koma ina jihohin kasar ke shirin su bi a cikin neman biyan bukatar karbar tsofafi na kudin dai, ra'ayi yana rabe ko a cikin lauyoyin bisa fassarar umarnin da tai nasarar ruda daukacin tsari na kudi na kasar. Koma a ina matsayar shari'ar take a tunanin lauyoyin kasar, shi kansa zuwa kotun kolin dai a fadar Barrister Saidu Tudun Wada da shi kansa umarnin kotun na zaman kuskuren da ke dada jefa al'umma cikin rudani yanzu. Ko bayan rudanin talakan dai hauma-haumar daga dukkan alamu ta tsallaka zuwa ga jihohi, inda jihohin Edo da Bayelsa suka tsoma kafa cikin shari'ar tare da nuna goyon bayansu ga gwamnatin tarrayar.