Amfani da na'urar BVAS a zaben Najeriya
February 1, 2023Kama daga 'yan kallon cikin gida zuwa na kasashe na waje da uwa uba masu siyasa ta kasar, hankali yana ta karkata zuwa na'urar fasahar BVAS din a cikin neman ingantar zaben a tsakanin miliyoyi na 'yan kasar.
Kasa da makonni hudu da kai wa ya zuwa babban zabe, hankalin miliyoyin 'yan Najeriya ya kara karkata zuwa amfani da na'urar BVAS a kokarin tabbatar da ingantaccen zabe a kasar. Kuri'a kusan dubu dari ce dai wata kotun zabe a jihar Osun ta ce, ta baci sakamakon banbancin da ke tsakanin tantattun 'yan zabe da yawan kuri'ar da aka kidaya a zaben gwamnan jihar na shekarar da ta shude.
A wani abin da ke dada nuna irin sauyi da 'yan kasar ke fatan su gani a cikin tsarin zabe na kasar a lokaci mai nisa. A cikin tsakiyar sabon fatan dai, na zaman fasahar na'urar BVAS da tanadi tantancewar 'yan zabe da fasahar ta zamani, kafin kai wa ya zuwa kadin kuri'ar mai tasiri.
To sai dai kuma in har BVAS ta burge jam'iyyar PDP ta masu tsintsiya a jihar Osun, can a jihar Ekiti dai tsarin ya gaza kai wa zuwa biya na bukatar SDP da tazo ta biyu a zaben gwamna na jihar. Jam'iyyar kuma a fada ta shugabanta Shehu Gabam, matsalar ta fasaha na a wuyan masu sarraffata, maimakon tasirinta cikin harkar zaben.
Tarrayar Najeriyar dai tayi kaurin sunan rikicin zaben da a lokuta da daman gaske kan fara daga zargin aringizon kuri'u yayin zaben da kan zamo ruwan dare game duniyar kasar. Shi kansa shugaban kasar Muhammadu Buhari, bai boye aniyar amfani da fasahar da nufin iya kai wa ya zuwa zaben da 'yan kasar dama bakinta ke iya kai wa ga yabawa.