Najeriya: Kalubalen tsaro da barazanar yunwa
July 21, 2021A wani abun da ke zaman babbar barazana ga wadata ta abinci, batun rashin tsaron da ke tashi da lafawa na tilastawa manoma kauracewa gonaki da jefa daukacin Najeriya cikin hali na rashin tabbas ga kokari na ci da kai.
Karin Bayani: Najeriya: Muhawara ta barke a kan batun tsaro
Duk da cewa, yanayin na zaman na bikin Sallar layya, daga dukkan alamu hankali na tashe tsakanin sarakuna dama talakawa na arewacin kasar da ke ta korafin tana nuna alamu na baki ga makoma ta ci da kan al'umma a cikin yankin. Kuma kama daga Sultan na Sokoto ya zuwa sarakunan na arewa, babban sakon Salla na zaman kara kulawa a cikin tasirin na tsaro da ke barazana ga makoma ta abinci cikin yankin da mafi yawan al'ummarsa ke zama na manoma.
Karin Bayani:Najeriya: Bukatar dakatar da tashin hankali
Rashin tsaron da ya mamaye sasssan Arewa maso Yammacin kasar da ta tsakiya, ya tilastawa manoman mantawa da sana'ar gado da nufin ceto rayuwar da ke fuskantar barazana a halin yanzu. Kafin ta'azzarar rikicin rashin tsaron, masu mulkin Najeriya sun yi nisa a kokarin wadata kai da abincin da ya kai kasar zama ta kan gaba a noman shinkafa. Ya zuwa karshe na shekarar 2019, Najeriyar ce ta samar da kaso 55 cikin dari na tan miliyan kusan 15 da nahiyar Afirka, kafin karkatar tsaron da tasirinsa cikin harkar noma.
Duk da cewa, daminar na dada nisa kuma tasirin rashin tsaron yana ta bayyana ta ko'ina, har ya zuwa yanzu akwai sauran fata a fadar Bello Matawalle da ke zaman gwamnan Zamfara, daya kuma cikin jihohin da ke ji har a kwakwalwa bisa tasirin rashin tsaron cikin harkar noma. Kafin sabon shirin gwamnatin Najeriya na ci da kai da ke zaman babban kwazo, kasar na kashe dubban miliyoyi na daloli wajen shigo da kaya na abinci daga kasashe na waje.