1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawo kan matsalar tsaron Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 14, 2021

Kama daga yankin Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma a Najeriya, matsalar tsaro na kara ta'azzara tare da neman gagarar kundila.

https://p.dw.com/p/41hWK
Cartoon Nigeria Sicherheit Lage
'Yan bindiga kan wkashe mutane, tare da shiga daji da su domin su nemi kudin fansa

An dai kai ga katse hanyoyin sadarwa da layukan waya a jihar baki dayan jihar Zamfara, sakamkon matsalar 'yan bindiga da ke sace mutane su shige da su cikin dazuzzuka tare da neman makudan kudin fansa. Haka dai jihohin Kaduna da Katsina da Sokoto dukkansu a yankin Arewa maso Yamma da kuma jihohin Niger da Plateau a Arewa maso Tsakiya, ke fama da irin wannan matsalar. Yankin Arewa maso Gabashi musamman jihar Borno da Yobe kuwa, sun kwashe tsawon shekaru yana fama da matsalar 'yan ta'addan Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a Najeriyar da makwabtanta. 

Haka abin yake a yankin Gabashin kasar da ke fama da hare-haren 'yan kungiyar IPOB da ke neman ballewa daga Najeriyar su kuma kafa kasarsu ta Biafra. Rahotanni sun nunar da cewa shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bukaci ma'aikatar tsaron kasar da ta fara kera makamai samfurin gida, domin tallafawa na wajen da ba sa isarta a yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai, kana shugabannin al'umma da addini na ta kiraye-kirayen ganin an samu zaman lafiya musamman a bangaren rikicin kabilanci da na addini da kan barke na da can a kasar.