1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

CBN zai samar da eNaira a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
September 30, 2021

Babban bankin Najeriya na shirin kadammar da eNaira wato tsarin kudi ta internet, wanda za a rinka amfani da shi a kasar da ma sauran kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/4170l
Währung Nigerianischer Naira Zeichen
Ko kaddamar da sabon kudi na eNaira zai taimaki tattalin arzikin Najeriya?Hoto: Colourbox

Kudin na eNaira da ake shirin kaddamar wa a Najeriyar dai, nau'i ne na kudin Crypto da yake tashe a duniya. Babban bankin Najeriyar dai tuni har ya kadammar da shafin internet na kudin da aka yi wa lakabi da eNaira, inda daukacin hada-hadar da za a rinka yi ta saye da sayarwa za ta kasance ta kafar intanet. An bullo da wannan nau'in kudi ne a daidai lokacin da Najeriyar ke kara kaimi wajen amfani da internet domin hada-hadar kudi da nufin rage yawo da su a hannu. Babban bankin Najeriyar wato CBN dai, ya bayyana cewa kudin internet na eNaira ba wai zai maye gurbin takardar kudi ta Naira ba ne.

Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Za a ci gaba da amfani da Naira ta takarda, bayan kaddamar da eNairaHoto: Getty Images

Sai dai ya nunar da cewa eNaira, za ta zama amintaciyyar hanya ta hada-hadar kudi a fannin saye da sayarwa da ma rike darajar kudin. Amfana ta fannin samun riba domin rage radadin koma bayan tattalin arziki ne kan gaba a zukattan 'yan Najeriya a kan wannan nau'in kudin Naira na intanet da ake shirin kadamarwa a ranar daya ga watan Oktoba da ta zo daidai da ranar bikin cikar Najeriya shekaru 61 da samun 'yanci. Najeriyar dai ta bullo da wannan kudi na internet na eNaira bayan haramta hada-hadar irinsa na Crypto a kasar, a yanayi mai kama da ta yi amai ta lashe. Tuni kwararru ke kashedin babban banki ya bi a hankali, saboda akwai kalubale a gaba.