Najeriya ta bukaci sojojin Nijar su saki shugaba Bazoum
December 3, 2023Najeriya ta bukaci sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar da su saki hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum domin tafiya wata kasar, idan har suna son a fara tattauna batun janye takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata.
Karin bayani:ECOWAS: Nazari kan dalilan juyin mulki a Afirka
Ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar ne ya yi wannan jawabi, yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channels, a daura da taron sauyin yanayi da ke gudana yanzu haka a Hadaddiyar Daular Larabawa.
A ranar 10 ga wannan wata na Disamba ne jagororin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS za su gudanar da taro na musamman a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, domin tattauna batutuwan da suka shafi juyin mulkin sojoji da yankin ke fama da shi.
Karin bayani:ECOWAS za ta yi taro kan matsalolin juyin mulkin sojoji a yankin
Yanzu haka dai kasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da kuma Jamhuriyar Nijar na hannun sojoji, yayin da wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Saliyo ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21 a makon jiya.