1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsofaffin sojoji za su yaki ta'addanci a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
June 22, 2022

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana shirinta na amfani da tsofaffin sojojin kasar da suka yi ritaya domin yakar ta'addanci, a kokarin yakar matsalar da ta addabi kasar da makwabtanta.

https://p.dw.com/p/4D5eK
Najeriya I Sojoji I Sintiri I Tungushe
Najeriya dai ta kwashe tsawon shekaru cikin matsalar ta'addanciHoto: AFP/Str

Yanke shawarar amfani da tsofaffin sojojin da suka yi ritaya a Najeriyar domin su taimaka a yaki da matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar dai, ana masa kallon wata dabara ce ta amfani da kwarewa da ma cancantarsu a fannin. Babban hafsan sojojin Najeriyar Laftanar Janar Farouk Yahya ya ce kwararru da suka yi fice a aikinsu wadanda suka yi ritaya cikin sojojin, za a sake nemo su domin su yi aiki a kokarin fitar da Najeriyar daga wannan hali da ya kai wa kowa a wuya. Kama daga yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar da ake fama da ta'addanci da garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yammaci da yake naso zuwa sauran sassan kasar.

Najeriya | 'Yan Gudun Hijira I Pulko
Dubban mutane ne dai, matsalar ta'addanci ta raba da muhallansu a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Kama daga kwararru a fannin tsaro zuwa ga tsofaffin sojoji a kasar, an dade ana kiraye-kiraye ga Najeriyar da ta yi amfani da kwarewarsu wajen taimakawa a yaki da 'yan ta'addan sanin cewa mafi yawansu an musu ritaya tun suna da sauran karfi da ma kwarewarsu ta aiki a Najeriyar da kasashen waje. Gwamnatin Najeriyar dai ta kawar da batun yin hayar mayaka daga kasashen waje, tun bayan takaddamar da wannan ya haifar a lokacin gwamnatin da ta gabata. Ana yabawa wannan shawara a yanzu, koda yake Najeriyar na da dimbin matasa da ba su da aikin yi a kasar wadanda sanya su a irin wannan aiki na iya taimaka rage matsalar. An dade dai ana kiraye-kiraye na amfani da matasa a irin wannan harka, musamman wadanda suka shiga aikin sa kai na JTF da suka dade suna taimakawa jami'an tsaro a fanoni da dama na yaki da matsalolin rashin tsaron.