1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan fasa zuwan Buhari Zamfara

January 27, 2022

Al'ummar jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya mai fama da matsalar tsaro, na mayar da martani bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya fasa kai ziyara jihar.

https://p.dw.com/p/46CZe
Faransa Paris | Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: JULIEN DE ROSA/AFP/Getty Images

Tun da fari dai an shirya cewa Shugaba Muhammadu Buharin zai kai ziyarar aiki Sakkwato da Zamfara, jihohin da dukkansu ke fama da hare-haren 'yan bindigar daji masu kona garuruwa da sace mutane domin karbar kudin fansa a yankin Arewa maso Yammacin Najeriyar. Sai dai kuma ziyarar ta Shugaba Buhari ta togace a jihar Sakkwato kawai, inda aka ce matsalar yanayi ta sanya ba zai samu damar isa makwabciyarta Zamfaran ba.

Zanga-zangar nuna damuwa da rashin tsaro a Zamfara
Zanga-zanga kan matsalar tsaro a jihar Zamfara da ke NajeriyaHoto: DW/Yusuf Ibrahim Jargaba

Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle ne dai ya sanar da fasa zuwan shugaban kasar, a daidai lokacin da al'umma ke dakon zuwansa tsawan sa'o'i da dama. Da dama daga al'ummar Zamfaran na ganin ya kamata ace shugaban ya sauya dabara ya  karasa jihar tasu da tun da fari ya kudiri aniyar zuwa ganin yadda suke fama da matsalar tsaro, sai dai mahukunta sun bai wa al'umma hakuri tare da ba su tabbacin cewa Shugaba Bahari zai shirya wata ziyarar zuwa jihar ta Zamfara a nan gaba kadan.