Dangote na zargin yi masa zagon kasa
June 24, 2024Duk da cewa dai tun kusan watan Janairun da ya shude ne matatar man ta Dangote ta fara aikin tace man, har ya zuwa yanzu mafi yawan danyen man da take tacewa na zama na kasashen da ke wajen Tarayyar Najeriyar. Matatar dai na zargin manyan kamfanonin da ke aikin hakar mai a kasar da yi mata zagon kasa, a kokarin samun man tace wa. Mataimakin shugaban kamfanin Davakumar Edwin dai ya ce a mafi yawan lokuta ko dai kamfanonin kan sanar da Dangoten ba danyen man na sayarwa, ko kuma kan kara farashi ya zuwa sama da abun da kasuwanni na duniya ke cewa.
Karin Bayani: Najeriya: An fara kai danyen mai zuwa matatar Dangote
Kamfanonin dai kan dora kuşan dalar Amurka shida kan kowace ganga ga kamfanin na Dangote, abun kuma da ke tilasta masa juya akala zuwa waje da nufin neman man tacewar. Tuni dai dama Dangoten ya fara nuna alamun da na sani, cikin shiga harkar tace man da ya ce tana a karkashi na tsiraru a duniya. Injiniya Mohammed Lawal dai na zaman tsohon dan kwamitin gudanarwa a kamfanin man Najeriyar na NNPC, kuma ya ce dama can ba da son kamfanonin aka kafa matatar da ke iya kai wa ga samar da 'yancin kasar cikin batun man fetur din ba. Matatar da ke iya tace ganga dubu 650 kullum dai na zaman irinta mafi girma a duniya, kuma na da karfin biyan bukatar makamashi ga daukacin Najeriyar.
A karkashin dokokin masana'antar mai ta kasar matatar Dangoten a fadar Dakta Garba Malumfashi da ke zaman kwararre kan batun makamashin, na da ikon samun man kafin kai shi zuwa ga kasuwanni na duniya. Babbar matsala dai ya zuwa yanzu na zaman ta cefanar da danyan man Najeriyar tun ma kafin kai wa ga hako shi, abun kuma da ya bai wa kamfanonin damar kaucewa dokar da kila ma yin na gaban kai cikin cinikinsa. To sai dai kuma gaza samun isasshen man tacewar, na nufin ci gaba da dogaro da tattacen mai na waje ga kasar da ke ta korafin rashi na kudade. Ya zuwa watan jiya Abujar ta ce ta biya abun da ya kai sama da Naira tiriliyan biyar da nufin tallafawa man fetur na waje, duk da ayyukan matatar ta Dangote.
Karin Bayani: Ana kwan-gaba kwan-baya kan janye tallafin man fetur
Sabon korafin kamfanin dai na nuna irin jan aikin da ke gaban kasar, wadda ke tunanin kai wa zuwa kwana cikin batun na man fetur amma kuma ke kallon kalubale mai girman gaske. Siyasar makamashi ta duniya dai a fadar Dakta Isa Abdullahi da ke zaman kwararre ga tattalin arziki, na zaman na kan gaba a kokarın rawar kamfananon da ke kallon Najeriya da idanu na kasuwa mafi girma a bangaren tataccen man a nahiyar Afirka. Ko bayan batu na arziki ba adadi dai, Najeriyar na kuma zaman kasuwa mafi girma a nahiyar Afirika da daukacin manyan kasashen duniya ke wasoso.