Nasarar APC a zaben jihar Edo na shan fasarra mabambanta
September 23, 2024Jami'an tsaro sun yi nasarar kwantar da zanga-zangar da ta barke sakamakon rashin jin dadin wasu 'yan jihar Edo kan alkaluma da hukumar zabe ta INEC ta fitar, inda ta ce dan takara Monday Okpebholo na jam'iyyar APC ne ya lashe zaben na gwamna. Hasali ma, rundunar tsaro na aikin sintiri a sassan birnin Benin da ke zaman hedikwatar jihar Edo da nufin tabbatar da zaman lafiya tare da tabbatar da cewar za su sa kafar wando daya da 'yan son tayar da fitina.
Karin bayaniJam'iyyar PdP ta Najeriya na cikin rudani:
Amma bayan da aka sanar da wanda ya lashe zabe, gwamnan Edo Godwin Obaseki da ke zaman dan jam'iyyar PDP, ya yi wa jama'ar jihar jawabi na kwantar da hankali, inda ya kara da cewa: "Abin sha'awa ga mulkin Dimukuradiyya shi ne yadda jama'a ke da 'yancin zaben wadanda suke son su mulke su, kuma idan har an yi kwacen wannan mulki, ba wai tashin hankali ne kadai ba, amma yanayi ne na karya dimukuradiyya, kuma abin bakin cikin shi ne wannan 'yanci na zabe, da a ka warcewa 'yan Edo da karfin tsiya ya dusashe karsashinsu na son Dimukuradiyya."
Kungiyoyin da su ka kalli zaben na Edo, irin su YIAGA Afrika da CDD West Afrika suka ce akwai damuwa kwarai kan batun tsare gaskiya da adalci a zaben Najeriya, bisa la'akkari da yadda zaben jihar Edo ya gudana. Hatta wasu daga jam'iyyu 16 da suka fafata sun bayyana rashin amincewarsu da yadda zaben ya gudana.
Karin bayani: Najeriya: Damuwa kan rashin siyasar akida
Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari da na yanzu Bola Ahmad Tinubu sun mika sakonsu na taya Jam'iyyar ta APC murnar lashe zabe a jihar Edo, lamarin da Shugaba Tinubu ya ce alama ce karara mai nunin cewar 'yan Najeriya sun gamsu da salon mulkin jam'iyyarsu a kasar.
'Yan asalin jihar Edo sun jyi tsakaci kan wannan zabe na gwamna, inda daya daga cikin su ke cewa: "Zabe ya zo ya tafi, kuma na yi farin ciki da abin da idona ya gwada min, domin 'ya'yan Edo biyu ne suka kara amma daya ya samu," Sai dai Uchechi na da ra'ayin da ya bambanta, inda ta ce: "Sun bayyana alkaluman zabe, ana maganar 'yanci na zabe, amma gaskiya, ba mu gamsu da sakamakon wannan zabe ba."