NATO na taro kan bai wa Ukraine makamai
May 31, 2024A yayin zaman taron, ana sa ran ministoci su tattauna kan sanarwar Shugaba Joe Biden na Amirka, na bai wa Ukraine damar amfani da wasu makaman kasar kan Rasha. Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yin kira kan a amincewa gwamnatin Kyiv, ta yi amfani da makaman da ake aikata mata wajen kai samame cikin Rasha.
Karin bayani: NATO za ta bai wa Ukraine karin makaman kakkabo jiragen yaki na sama
Sai dai akwai ayar tambaya da ake diga wa, kan wasu sharudda kasashe mambobin kungiyar NATO za su saka kan yadda Ukraine na amfani da makaman.
Babban sakataren kungiyar, Jens Stoltenberg ya ce akwai yiwuwar a dage wasu takunkumai na kai hari kan Rasha sakamakon yadda fada ke kara matsawa kusa da iyakar Ukraine. Sai dai gwamnatin Kremli ta ce a jira abun da zai biyo baya idan aka kaddamar da hari.