NATO za ta bai wa Ukraine karin makaman kakkabo jiragen yaki
April 19, 2024Kungiyar tsaro ta NATO ta amince da bai wa Ukraine karin tallafin makaman kakkabo jiragen yaki na sama, bayan mika kokon bararta da ta yi don samun damar harbo jiragen Rasha.
Karin bayani:Shekaru 75 da kafa kungiyar tsaro ta NATO
Sakatare Janar na kungiyar Jens Stoltenberg, wanda ya gana da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ta Intanet a Juma'ar nan, ya ce nan ba da jimawa ba za a ji irin taimakon da za su bai wa Ukraine na makaman kare kai.
Karin bayani:Ministocin NATO na taro kan shirin tallafa wa Ukraine
A farkon makon nan ne dai Jamus ta alkawarta bai wa Ukraine makami mai linzami na harbo jirgin sama, kari a kan wasu guda biyu da ta riga ta ba ta a baya. Inda Mr Stoltenberg ya bayyana cewa suna da irin wadannan makamai jibge.
Kasashen kawancen NATO da ke da irin wadannan makamai sun hada da Amurka da Jamus da Holland da Spain da Greece, sai Romania da kuma Poland.