1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro kan shirin sake gina yankin Tafkin Chadi

Gazali Abdou Tasawa RGB
January 23, 2023

A wannan Litinin aka bude babban taron kasa da kasa a birnin Yamai na kasar Nijar don nazari kan yadda za a sake gina yankin Tafkin Chadi da rikicin Boko Haram ya daidaita.

https://p.dw.com/p/4MbAf
Taro kan sake gina taflin Chadi a Nijar
Taro kan sake gina Tafkin Chadi a NijarHoto: Ali Abdou

A Jamhuriyar Nijar aka bude babban taron kasa da kasa kan batun sake gina yankin da rikicin Boko Haram ya daidaita. Taron wanda shi ne karo na uku da ake shiryawa a bisa daukar nauyin kasashen Jamus da Norway a karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya, zai yi bitar inda aka kwana a game da ayyukan ceto yankin da aka yi a baya da kuma bukatun da ya kamata a tunkara a yanzu.

A shekara ta 2017 ne kasashen na Jamus da Norway da Hukumar raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya watau PNUD da kuma Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya, suka assasa a karon farko wannan taro na nazarin hanyoyin sake gina yankin Tafkin Chadi wanda rikicin Kungiyar Boko Haram  da kuma sauyin yanayi suka daidaita. Bayan taro na biyu wanda birnin Berlin na kasar Jamus ya karbi bakuncinsa a shekara ta 2017, a bana Nijar ta karba.

Mataimakiyar Ministan harkokin wajen Jamus Katja Keul da Ministan harkokin wajen Nijar Hassoumi Massaoudou
Mataimakiyar Ministan harkokin wajen Jamus Katja Keul da Ministan harkokin wajen Nijar Hassoumi MassaoudouHoto: Ali Abdou

Taron na Nijar ya samu halartar tawaga daga kasashen guda hudu na yankin Tafkin Chadin da suka hada da Najeriya da Chadi da Libiya da Kamaru da kuma Afirka ta Tsakiya. Jamus wacce ke zama jagorar masu kawo tallafi a shirin ta bakin karamar ministar harkokin wajenta Madame Katja Keul tuni ta sanar da saka hannu a aljuhu domin talllafa wa shirin. Za a share kwanaki biyu ana gudanar da wannan taro inda daga karshe za a fitar da shawarwari na inganta tsarin na neman sake gina yankin na Tafkin Chadi wanda rikicin boko Haram da sauyin yanayi suka daidaita da kudaden da shirin ke bukata.