1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar dorewar zaman lafiya a Nijar

August 9, 2023

Tsofaffin 'yan tawayen Jamhuriyar Nijar, sun yi kira ga 'yan kasar da su yi kokari wajen kare martabarsu ta hanyar tattalin zaman lafiya da Allah ya ba su.

https://p.dw.com/p/4Uy1k
Jamhuriyar Nijar | Juyin Mulki | Tawaye | Agadez | Zamn Lafiya | Liman Ahar Fidajai
Shugaban kungiyar malamai mai shiga tsakani a Agadez Liman Ahar FidajaiHoto: Bettina Ruehl/epd/imago images

Tsofaffin 'yan tawayen Jamhuriyar Nijar din sun kuma bayyana cewa, hadin kai da kwanciyar hankali tare da nuna kin yarda ga duk wani abu da zai gurbata zaman lafiya da son junan da suke tinkaho da su. Sun kuma bayyana cewa za su yi iya nasu kokarin har sai inda karfinsu ya kare, wajen kawo gudummawa domin tabatar da zaman lafiya a kasar. Kasancewar tsofaffin 'yan tawayen sun san muhimancin zaman lafiya da kuma rashinsa, ya sa suke fatan talakawan Nijar su fita daga cikin matsalolin, inji guda cikin tsofaffin 'yan tawayen Adou Mbarik. A nasa bangaren, shugaban kungiyar malamai mai shiga tsakani da wanzar da zaman lafiya Liman Ahar Fidajai ya shaidawa DW cewa zaman lafiya na da matukar muhimanci. Sai dai furucin daya daga cikin jagororin tsofaffin 'yan tawayen kan juyin mulkin sojojin da ya yi na yunkurin kafa wata kungiyar gwagwarmaya da ma kira ga wasu kabilun kasar da su fito su dauki makamai su koma daji, ya soma tayar da hankali da ma saka fargaba a zukatan al'ummar kasar musamman ma a jihar Agadez.