1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Nijar na shirin yakar cin-hanci

Gazali Abdou Tasawa LMJ
September 22, 2023

Kungiyoyin Transparacy International reshen Jamhuriyar Nijar da wasu kungiyoyin kare hakin dan Adam, sun fara martani a kan matakin da Janaral Abdourahamane Tchiani ya dauka na kafa sabuwar Hukumar Yaki da Cin-hanci.

https://p.dw.com/p/4Wf6Y
Jamhuriyar Nijar | Janaral Abdourahamane Tchiani | Juyin Mulki | Bazoum Mohamed
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar Janaral Abdourahamane TchianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Sabuwar Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa da aka yi wa lakabi da COLDEF da shugaban mulkin sojan Jamhuriyar ta Nijar Janaral Abdourahmane Tchiani ya kafa dai, za ta mayar da hankali ga yaki da cin-hanci da kuma kwato dukiyar kasa da ake zargin wasu 'yan kasar sun wawure ba bisa ka'ida ba. Cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar Mulkin Sojan ta CNSP ya karanto a gidan radiyo da talabijn na kasa, ya sanar da wannan matakin. Da yake tsokaci kan wannan batu Malam Siraji Issa na kungiyar Mojen cewa ya yi sabon matakin yakar cin-hancin abin a yaba ne, amma kuma akwai yiwuwar allura ta tono garma in har ba a yi tsambare cikin aikin yaki da cin-hanci da tara dukiyar haram din ba.

Jamhuriyar Nijar | Sojoji | Cin-hanci | Yaki | COLDEF | HALCIA
Kokarin yaki da cin-hanci da rashawa a Jamhuriyar Nijar

A hakumance dai hukumomin ba su sanar da rusa kungiyar HALCIA shahararriyar Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta kasar ba, amma sabuwar hukumar ta COLDEF za ta yi irin aikin da HALCIA ke yi a Nijar din ne. To amma kungiyar ANLC reshen kungiyar Transparancy International a Nijar ta bakin shugabanta Malam Maman Wada ta ce, kafa sabuwar hukumar bai dace ba. Abin jira a gani shi ne tasirin da hukumar ta COLDEF za ta yi wajen yaki da cin hanci da rashawar, la'akari da yadda ilahirin gwamnatoci na soja ko na farar hula da suka mulki Nijar tun daga shekara ta 1990 kawo yanzu ba wadda ba ta kafa tata hukumar yaki da cin-hanci a kasar ba.