1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na neman karin lokaci domin tattaunawa da ECOWAS

Salissou Boukari AH
January 8, 2024

A Jamhuriyar Nijar yayin da ake jiran tattaunawa tsakanin kungiyar ECOWAS da hukumomin kasar,gwamnatin ta nemi da kungiyar ta ECOWAS ta dan basu lokaci har su gudanar da babban taro na kasa.

https://p.dw.com/p/4b07J
Abdourahamane Tiani
Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

 Wasikar dai duk da cewa ba wasika ba ce da aka so ta yadu haka ba, shugaban gwamnatin ta Nijar ya rubuta wa ministan harkokin wajen kasar Togo ne ganin cewa Togo dai na a matsayin mai shiga tsakani kuma menba a kwamitin tattaunawa na tsakanin Nijar din da ECOWAS don ganin Nijar din ta samu gudanar da tattaunawar da take shirin yi da bangarorin kasar don samar da cikaken tsari na tafiyar mulkin rikon kwarya musamman ma dangane da wa'adin da 'yan kasar ta Nijar ke son a dauka na tsawon mulkin  rikon kwarya.

Shugaban mulkin soji na Nijar ya tattauna da Tinubu jagoran ECOWAS

 Bola Tinubu
Bola TinubuHoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Tuni dai a bangaran masu goyon bayan hambararran shugaban kasar ta Nijar Mahamed Bazoum ta bakin Sahanine Mahamadou ake gannin lamarin na gwamnatin à matsayin jan kafa don kar su saki tsahon shugaban da iyallansa kaman yadda yake cikin ka'idojin kungiyar ta  ECOWAS. Sai dai a daidai wannan lokaci dsa ake batun neman kungiyar ta ECOWAS ta dakata da wannan tattaunawa har a kammala taron na kasa a Nijar, akwai kuma wata wasika da ke yawo ta shafukan sada zumunta da ake nuni da tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaban kungiyar tarayyar Afirka da shugaban kasar Nijar na mulkin sojal, batun da har yanzu ba mu kai ga samun tabbacinsa ba daga bangaran fadar shugaban kasar na Nijar ba. Sai dai da yake magana kan wannan batu Mamane Bachar dan kungiyar farar hula mai shari kan harkokin yau da kullum na ganin cewa wannan ba wani sabon batu ba ne idan aka yi la'akari da jawabin shugaban kasa Abdourahamane  Tianiinda ya tabo wannan batu a cikinsa.

Ko ECOWAS za ta aminta da shawarwarin taron kasa

Nigeria | ECOWAS-Staatsoberhäupter in Abuja 2023 | Regionale Zusammenarbeit
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Abun da kowa ke jiran gani dai shi ne yadda wannan zaman taro na 'Yan kasar ta Nijar zai gudana, inda kowa ya zura idanu ya ga iri-irin matakan da za a dauka na ganin a tsaida cikakar kilbla ta mulkin rikon kwarya a kasar ta Nijar. Wanda ba lalle ne bai ta kungiyar ECOWAS ta aminta da matakan da taron zai dauka musamman ma a fannin wa'adin mulkin narikon kwarya.